Izala ta taimaka wa ’yan Dambowa da ke gudun hijira a Gombe

kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a wa’ikamatus Sunnah ta kasa reshen Jihar Gombe ta kara taimaka wa ’yan Dambowa da ke gudun hijira a Jihar Gombe bayan ta ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar a makon jiya.A yayin ziyarar ne Shugaban kungiyar Izalar reshen jihar Gombe Injiniya Salisu Muhammad Gombe ya bayyana takaicinsa sakamakon halin tagayyara da ’yan […]

Izala ta taimaka wa ’yan Dambowa da ke gudun hijira a Gombe
Izala ta taimaka wa ’yan Dambowa da ke gudun hijira a Gombe

kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a wa’ikamatus Sunnah ta kasa reshen Jihar Gombe ta kara taimaka wa ’yan Dambowa da ke gudun hijira a Jihar Gombe bayan ta ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar a makon jiya.
A yayin ziyarar ne Shugaban kungiyar Izalar reshen jihar Gombe Injiniya Salisu Muhammad Gombe ya bayyana takaicinsa sakamakon halin tagayyara da ’yan gudun hijirar suka shiga, sannan ya bukaci a dauki al’amarin a matsayin jarrabawa daga Allah.
Shugaban ya ce baya ga wadannan al’umma da suke sansanin gudun hijira, wanda yawansu ya kai mutum dubu uku, akwai wadanda suka kama haya a cikin gari, saboda suna da ikon yin hakan.
Ya ce: “Wadanda suke haya a cikin gari ma mun sanya a bincika adadinsu domin a tallafa musu, sannan za mu ci gaba da ba da irin wannan tallafi har lokacin da za su koma gidajensu.”
Da yake tsokaci kafin mika kayayyakin  Shugaban Rundunar ’yan agaji na jihar Alhaji Usman Maigari Malala, ya ce kungiyar za ta rarraba kayayyakin ne a matsayin dauki bisa halin da ’yan gudun hijirar suke ciki.
kungiyar ta mika kayayyakin ga hukumar ba da agajin gaggawa ta SEMA don ta raba wa ’yan gudun hijirar.
Kayayyakin sun hada da tufafi na maza na mutum dari 800 da na mata dari 750 da na yara a buhunhuna goma, sannan akwai hijabi na mata da takalma na maza da mata da huluna  da sabulan wanki da na wanka da Omo katan goma da kuma taburman leda.
Sauran kayayyakin sun hada da Al’kur’anai da kayan abinci da suka hada da garin masara buhu 10 da buhun shinkafa shida da kayayyakin aikin cikin gida da sauransu.
Da take karbar wadannan kayayyaki a madadin hukumar SEMA da kuma NEMA, Daraktar Hukumar SEMA Hajiya Laraba Ahmed Kawu, ta mika godiya ga kungiyar  Izala sakamakon taimaka wa ’yan gudun hijirar da take yi, inda ta ce in Allah Ya yarda za su raba kayayyakin yadda suka dace ga wadanda abin ya shafa.
Ta  kara jinjina wa kungiyar ta Izala kan tsarin da ta bullo da shi na tallafa wa wadanda suke haya a cikin gari.
Ta bukaci sauran kungiyoyi su yi koyi da Izala wajen kawo wa ’yan gudun hijira tallafi saboda halin rayuwar da suke tsinci kansu a ciki.
Wannan shi ne karo na biyu da kungiyar take kai tallafin kayayyakin ga ’yan gudun hijirar a sansaninsu da ke bayan gari kan titin bye-pass.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno