Izala ta taimaka wajen inganta karatun Alkur’ani a Najeriya – Sheikh Sa’idu Jingir
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Biyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa kuma Sa’in kungiyar na kasa Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya ce kungiyar ta taimaka wajen inganta karatun Alkur’ani Mai girma a Najeriya. Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude musabakar […]
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Biyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa kuma Sa’in kungiyar na kasa Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya ce kungiyar ta taimaka wajen inganta karatun Alkur’ani Mai girma a Najeriya.
Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude musabakar karatun Alkur’ani Mai girma karo na 18 na kungiyar reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato a garin Jos.
Ya ce kafin bayyanar kungiyar a Najeriya, mutane da dama suna karanta Alkur’ani ne yadda suka ga dama. Amma da kungiyar ta bubbude makaratu tare da fara koya wa jama’a tajawidi sai aka samu gyara kan yadda ake karatun Alkur’ani yadda ya kamata.
Sheikh Sa’idu Jingir ya yi kira ga mahaddata Alkur’ani su yi kokari su rika rubuta shi, “Idan mahaddacin Alkur’ani ya rubuta shi zai dade haddarsa ba ta rushe ba. Kuma wajibi ne a kullum mahaddacin Alkur’ani Mai girma ya karanta aya 100,” inji shi.
Ya ce karatun Alkur’ani yana da matukar muhimmanci domin Allah Ya yi alkawarin zai ba mai karatun Alkur’ani dukkan abin da yake bukata.
A jawabin shugaban majalisar malaman karamar hukumar, Ustaz Muhammad Haris Shehu ya yi kira ga ’yan takarar gasar su yi kwazo kuma su tabbatar sun yi gasar
tsakaninsu da Allah.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi kokari su tallafa wa karatun Alkur’ani Mai girma, domin Alkur’ani shi ne babban littafin al’ummar Musulmi.
Tunda farko a jawabin Ko’odinetan gasar Hafiz Abbas Ahmad ya ce gasar wadda za a yi mako daya ana gudanarwa ’yan takara maza da mata 129 ne za su fafata a matakai daban- daban.