Izala ta tura malamai 485 don gudanar da tafsiri a bana
Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce kungiyar a matakin kasa ta tura malamai masu tafsiri 485 zuwa sassan Najeriya da kasashen makwabta. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka a lokacin da yake bude tafsirin da yake gabatarwa, a garin Jos a […]
Shugaban Majalisar Malamai ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce kungiyar a matakin kasa ta tura malamai masu tafsiri 485 zuwa sassan Najeriya da kasashen makwabta.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka a lokacin da yake bude tafsirin da yake gabatarwa, a garin Jos a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce, kungiyar a jihohi da kananan hukumomi ta tura daruruwan masu tafsiri, kuma ya bukaci su isar da sakon Allah a wuraren da aka tura su.
Sheikh Jingir ya yi kira ga ga ’yan kasuwa da mawadata su taimaka wa marasa shi a wannan wata na Ramadan. “Ku ’yan kasuwa ku sassauta kayan masarufi a wannan wata, masu hali kuma ku taimaka wa marasa shi, ku taimaka wa marayu da abinci da tufafi. Musulmin Najeriya mu taru a hada kai kan Alkur’ani domin shi ne gaskiya. Idan muna son hada kai da zaman lafiya, to mu hada kai kan gaskiya wato Alkur’ani Mai girma,” inji shi.
Sheikh Jingir ya shawarci ’yan Najeriya cewa kada su yi garaje kan sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, maimakon haka su ci gaba da yi mata addu’a.Ya ce ya kamata su fahimci cewa daga hawanta yanzu ba a kai wata ba, amma Shugaban kasa na kokarin hada kan kasashen makwabta don magance matsalar Boko Haram.
Ya yi kira ga ’yan majalisun dattawa da ta wakilai da majalisun jihohi su dauki darasi daga wadanda suka gabace su. “Ku fitar da son dukiya daga zukatanku ku fifita son kasarmu Najeriya. Ku rika zama kuna tattauna abubuwan da suke damun al’ummar kasar nan,” inji shi.