Izala ta yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a Najerya

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasar SheikhAbdullahi Bala Lau ya yi Allah wadai da zubar da jinin al’umma da ke ci gaba da faruwa a kasar nan ba tare da wani dalili ba, musamman harin baya-bayan nan a Nyanya da ke kusa da Abuja.Shugaban wanda ya aiko da sakonsa daga Makka […]

Izala ta yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a Najerya
Izala ta yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a Najerya

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasar Sheikh
Abdullahi Bala Lau ya yi Allah wadai da zubar da jinin al’umma da ke ci gaba da faruwa a kasar nan ba tare da wani dalili ba, musamman harin baya-bayan nan a Nyanya da ke kusa da Abuja.
Shugaban wanda ya aiko da sakonsa daga Makka inda yake gudanar da Umara ta hannun Daraktan Labarai na kungiyar Izala ta kasa Malam Ali dan Abba, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa don kawo karshen aika-aikar da ke ci gaba da faruwa.
Shiekh Bala Lau ya kuma shawarci gwamnatin ta hada taron sarakunan Arewa da malaman addini don gabatar da addu’o’i na musamman saboda lalubo sahihiyar hanyar magance wannan mummunan bala’i da ke ci gaba da faruwa.
 Ya kuma bukaci mahalarta taron kasa su mai da akalar taron wajen shawo kan wannan mummunan al’amari da ya addabi kasar nan, domin al’amarin yana da ban tsoro a mayar da ran dan Adam tamkar na kiyashi.
Ya ce Musulunci addini ne na zaman lafiya da ba da kariya ga rayuka da dukiyoyi kamar yadda ya tabbata a yayin Hajjin Ban-Kwana inda Annabi Muhammad (SAW) ya yi hudubar da ta ratsa zukata idanu suka zubar da kwalla a ranar Arfa, ya ce: “Ku riki rayukan Musulmi da dukiyoyinsu bisa girmamawa da ba da kariya.”
Shugaban ya bukaci al’ummar Musulmi su ci gaba da addu’o’in alkunut a duk sallolinsu da yawaita tuba ga Allah tare da sanya tsammanin kyautatuwar al’amura da samun rahamar Allah da tausayawarSa.
Ya jawo ayoyi da suke nuna al’umma za ta iya samun kanta a irin wannan hali, amma kuma sai Allah Ya yi musu rahama su fice daga ciki.
Sai ya mika ta’aziyya da jaje ga wadanda suka rasu a harin ko suka jikkata tare da kira ga gwamnati ta taimaka wa wadanda suke kwance a asibitoci da magunguna.