Izala ta yi Allah wadai da yunkurin hallaka Buhari da Sheikh dahiru Bauchi
kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, ta yi Allah wadai da yunkurin hallaka ga tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da Sheikh dahiru Usman Bauchi a ranar Laraba ta makon jiya, ta hanyar kai musu harin bam a Kaduna, inda a sanadin haka mutane da dama suka rasu, yayin da wasu suka […]
kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, ta yi Allah wadai da yunkurin hallaka ga tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da Sheikh dahiru Usman Bauchi a ranar Laraba ta makon jiya, ta hanyar kai musu harin bam a Kaduna, inda a sanadin haka mutane da dama suka rasu, yayin da wasu suka samu raunuka.
Wata takarda da Daraktan Watsa Labarai na kasa na kungiyar Malam Ali dan Abba ya fitar a madadin Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta ce, “Wadanda ke da hannu a al’amarin ya kamata su san cewa kashe jagoran al’umma irin Janar Buhari ko na addini kamar Sheikh dahiru Bauchi ba zai kawar da abin da suke kai ba, sai ma ya kara karfafa shi ta hanyar samun karin mabiya.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kuma mika ta’aziyyar kungiyar ga iyalan wadanda suka rasu a sanadin hare-haren biyu, kuma ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta rungumi salon rigakafin magance fadawa cikin akidar ta’addanci, ba yakarsa kawai ba.
Ya yi kira ga ’yan siyasa su guji siyatantar da matsalar ta’addanci, inda ya bukace su hada kai wajen tunkararsa a matsayin bala’i ga al’ummar kasa baki daya.
kungiyar ta kuma yaba wa kungiyar Likitoci na kasa reshen Jihar Kaduna da suka garzaya zuwa asibitocin gwamnati da ke birnin duk da yajin aikin da suke yi don ba da gudunmawarsu ga wadanda harin ya shafa. Ya bukaci Gwamnatin Tarayya da kungiyar ta kasa, su kawo karshen matsalar yajin aikin likitocin don magance matsalar da miliyoyin ’yan Najeriya ke ci gaba da fuskata a fannin kiwon lafiya.