Izala za ta aurar da zawarawa 200 kafin azumi
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce kungiyar tana shirye-shiryen aurar da zawarawa da ’yan mata 200 kashi na farko kafin watan azumin bana, a matsayin daya daga cikin gudunmawarta wajen rage yawan marasa aure a cikin al’umma.Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sanar da haka ne […]
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce kungiyar tana shirye-shiryen aurar da zawarawa da ’yan mata 200 kashi na farko kafin watan azumin bana, a matsayin daya daga cikin gudunmawarta wajen rage yawan marasa aure a cikin al’umma.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sanar da haka ne yayin da yake ganawa da wakilinmu a ofishinsa, inda ya ce tuni aka zakulo wadanda ake yi wa gwaje-gwajen da suka dace kamar yadda addinin Musulunci ya tanada domin auna kaifin hankalin wadanda za su ci gajiyar shirin. Ya ce za a dauke wa mazaje nauyin sadaki, su kuma mata kayan daki da duk abin da ya dace ma’auratan su samu.
Shugaban ya ce kungiyar tana samun kira daga wasu bayin Allah masu hannu da shuni da suke da muradin samun lada don taimaka wa wadanda suka kai munzalin yin aure, su yi a cikin lokaci.
Ya kara da cewa, “A yanzu haka, mun samu wasu bayin Allah daga jihohin Katsina da Kebbi da suka nemi mu jagoranci aurar da zawarawa da ’yan matan da ke yankunansu, sai dai za mu fara ne da Jihar Katsina a kashi na farko, da yake mun kusa kammala abin da ya dace dangane da shirye-shirye kafin azumin Ramadan na bana.”
Ya ce mata a wannan zamanin, sun fi kowa bukatar taimako, saboda yawancin wadanda suke rayuwa a cikin tasku mata ne, musamman wadanda mazajensu suka rasu, suka bar su da yara kanana.
Sheikh Lau ya ce daya daga cikin matakan da suke dauka domin dorewar wannan aure shi ne, ilimantar da ma’auratan darussan da suka shafi zaman aure da yadda ya kamata miji ya yi tattalin matarsa da yadda mace za ta yi tattalin mijinta bisa koyarwar addini kamar da yadda Annabi (SAW) ya nemi mabiyansa su yi.
“Bayan haka za a koya wa matan 200 sana’o’in da za su zama hanyar rufa musu asiri, kuma babbar manufarmu da wannan shirin shi ne, kada kowane daga cikin wannan aure da za a gudanar ya mace, muna son irin wannan ya zama abin koyi ga sauran jama’a ta yadda duk abin da za a yi, a yi shi bisa tsarin addini tsantsa,” inji shi.
Ya yaba wa gwamnonin Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da na Sakkwato Aliyu Magatakarda Wammako da na Gwambe Alhaji Hassan dankwambo da na Kaduna Alhaji Mukthar Ramalan Yero da suka assasa irin wannan sunnah mai kafi na taimaka wa marasa karfi samun abokan zama cikin sauki a jihohinsu.