Izala za ta hada kai da ’yan kasuwa don sayar da kayan masarufi a Ramadan

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta bayyana cewa baya ga kayan masarufi da ta saba karba daga al’umma don ba da su sadaka a lokacin Ramadan, za ta samar da kafa don hada gwiwa da ’yan Kasuwa da suka rage farashin hajjarsu don sayar da su ga al’umma a watan na azumi. […]

Izala za ta hada kai da ’yan kasuwa don sayar da kayan masarufi a Ramadan
Izala za ta hada kai da ’yan kasuwa don sayar da kayan masarufi a Ramadan

 Wani sashi na Malamai da ’yan kasuwa a yayin taronkungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta bayyana cewa baya ga kayan masarufi da ta saba karba daga al’umma don ba da su sadaka a lokacin Ramadan, za ta samar da kafa don hada gwiwa da ’yan Kasuwa da suka rage farashin hajjarsu don sayar da su ga al’umma a watan na azumi.
Shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a yayin taron bita da kungiyar ta shirya wa malamanta da za su yi tafsiri a masallatan kasar nan da kuma na makwabtan kasashe a lokacin azumin watan Ramadan da ke tafe.
A yayin taron wanda ya gudana a masallacin kasa na Abuja a ranar Juma’a da kuma Asabar da suka gabata, ya ce kungiyar za ta gudanar da tsarin ne ta bangaren kafarta na  “Manara” wanda ke tattara kundin al’amura na kungiyar da ke da kwamitoci a masallatan da ke karkashinta, wajen dubu tara a sassa daba- daban na Najeriya.
Ya bukaci kamfanoni da daidaikun ’yan kasuwa da ke da niyyar rage farashin hajojinsu da su hada kai da kafar tata, don taimaka wa al’umma marasa galihu musamman a watan azumi.
A jawabinsa Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan daga Kano, wanda ya yi bayani a kan Zakkah, ya ce mai bayar da Zakkah na ribatuwa da dumbin alheri fiye da mai karbarta, saboda Allah Zai kare dukiyarsa daga bala’i, ya jefa kaunar al’umma a gare shi, sannan ya bude masa karin kofofin samu a kan wanda yake da su.
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina ya bukaci malaman da su ka halarci bitar da su karfafa wa’azi a kan Tauhidi, karfafa Sunnah da kuma watsi da bidi’a, wanda ya ce shi ne babban akidar kungiyar.
A karshen taron shugaban kungiyar ya rarraba takardun da ke nuna inda Malami zai gudanar da tafsiri ga wasu daga cikin mahalarta taron, sannan ya bukaci shugabannin jihohi da su tsara na ragowar malaman a matakan jihohinsu, tare da sa’ido a kan yadda suke gudanar da shi.
Ya gargadi malaman da za su gudanar da tafsirin su nisanci nuna goyon bayansu ga wata jam’iyyar siyasa a lokacin tafsirin, kasancewar ba wadda aka kafa a tsarin musulunci, sai dai ya ce a madadin hakan su bukaci al’umma su zabi jama’a nagari da za su yi wa jama’a aiki da kuma kare musu muradu.