Ja-in-ja ke janyo tsinkewa

Zaben shugabannin Majalisun kasa guda biyu a ranar Talatar da ta gabata ya kawo karshen hada-hadar kakkafa tsarin gudanar da sha’anin mulki bayan zabubbukan da aka yi a watannin Maris da na Afrilu. An zabi Sanata Bukola Saraki daga jihar Kwara da kuma Hon Yakubu Dogara daga jihar Bauchi a matsayin sabbin shugabannin majalisun. Wannan […]

Ja-in-ja ke janyo tsinkewa
Ja-in-ja ke janyo tsinkewa

Zaben shugabannin Majalisun kasa guda biyu a ranar Talatar da ta gabata ya kawo karshen hada-hadar kakkafa tsarin gudanar da sha’anin mulki bayan zabubbukan da aka yi a watannin Maris da na Afrilu. An zabi Sanata Bukola Saraki daga jihar Kwara da kuma Hon Yakubu Dogara daga jihar Bauchi a matsayin sabbin shugabannin majalisun. Wannan ne lokaci na farko da aka taba samun Shugaban Majalisar Dattijai da mataimakinsa daga jam’iyyu daban-daban, kamar yadda aka samu tsohon mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu, dan jamiyyar PDP daga jihar Anambra ya sake komawa kan mukaminsa na tsohuwar Majalisar da ta shude.

Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bijirewa da wasu ‘yan tsirarun wakilan Majalisar Dattijai na jam’i yyar APC suka yi a karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki wanda ya nemi goyon bayan ‘ya’yan jam’iyyar PDP a Majalisar Dattijai don zamewa sabon shugabanta, ya kuma amince da tagaza ma wani daga jam’iyyar don zama mataimakinsa. To da yake a wannan Majalisar bambancin wakilan da ke tsakanin jam’iyya mai rinjaye, watau APC da kuma ta adawa, PDP guda goma ne kadai, sai ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta APC suka dunkule, suka bayar da cikakken goyon baya ga Sanata Bukola, kuma tun da an samu baraka ko a ce rashin hadin kai tsakanin zababbun Dattijan Majalisar na APC sai kawai su Bukola Saraki suka samu galba cikin ruwan sanyi. Irin abin da ya kuma faru ke nan a Majalisar Wakilai ta tarayya inda nan ma ‘ya’yan jam’iyyar PDP suka bayar da gudumawa ga wani fandararren dan jam’iyyar APC, Honorabil Yakubu Dogara har ya kai ga zama Shugaba.
Wannan al’amari bai yi wa uwar jam’iyyar APC dadi ba domin kuwa ta so ne a ce wasu ‘ya’yanta guda biyu da ta shafe da mai tun da farko , Sanata Ahmed Lawal daga jihar Yobe da kuma Honorabil Femi Gbajabiamila ne suka samu galba a zaben shugabannin Majalisun da ‘ya’ya suke da hakkin gudanarwa. Shi ya sa jim kadan bayan an fitar da sakamakon zabubbukan jam’iyyar APC ta fitar da wata sanarwa dauke da sanya hannun Babban Kakakinta, Alhaji Lai Muhammad, wacce a ciki ta yi tir da Allah-wadai da sakamakon, ta kuma nuna rashin jin dadinta game da yadda wasu ‘ya’yanta, suka biye son zukatansu a maimakon su yi la’akari da matsayin jam’iyya da kuma abin da ya fi zame wa kasar alheri. To amma Shugaba Muhammadu Buhari, wanda tun da farko ya nuna cewa zaben shugabannin Majalisun kasa hakki ne na ‘ya’yan Majalisun, ba kuma zai tsoma bakinsa ba a cikin al’amarin, ya nuna amincewarsa da sakamakon zabubbukan, yana mai cewa shi zai iya yin aiki da dukkan wanda ya samu nasara.
To amma wannan al’amari ya yi kama da ihu bayan hari ne, domin kuwa an rigaya an samar da shugabannin Majalisu, kuma bai kamata ba a ce shugabannin jam’iyyar na yi wa ‘ya’yanta bi-ta-da-kulli ba. Ana iya cewa aikin gama ya gama duk kuwa da cewa bisa ga dukkan alamu Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma shugabannin jam’iyyarsa sun raba gari, ko kuma a ce sun fara zaman ‘yan marina, kowa da inda ya sanya gabansa. Wannan ya nuna ke nan cewa an yi wa jam’iyyar APC juyin mulki a majalisa, kuma hakan na iya jefa Shugaba Buhari cikin babban hatsari idan har hakan ya kai ga tabarbarewa. Dalili kuwa shi ne an samu gungun wasu ‘yan adawa da ke da daurin gindin wakilan jam’iyyar PDP a Majalisun wadanda za su rika takawa kudurori da manufofinsa birki.Kuma sai an yi da gaske za su iya sakar masa mara har ya fitsare dangane da ayyukan da zai gudanar wadanda lallai sai ya nemi amincewarsu.
Jama’a na kallon wannan al’amari ta fuskoki da yawa. Wasu sun tabbatar da hakan shi ne mafi a’ala ga tsari irin na dimokradiyya, domin kuwa ga shi nan an ba al’ummomin jihohin Gabas babban mukami a Majalisar Dattijai wanda zai kwantar masu da hankali ganin cewa sun cire rai daga samun irin wannan mukamin domin tun da farko ba su zabi jam’iyyar APC ba. Sa’annan kuma zaben shugaban Majalisar Wakilai zai faranta wa al’ummomin shiyyar Arewa-ta-tsakiya, watau Middle Belt, musaman ma Kiristocin cikinsu ganin nasu ne ya samu wannan mukamin. Ana jin cewa hakan zai sa su mika wuya ga wannan gwamnatin, a kuma tafi tare da su yadda ya kamata.
Ta wani bangaren kuma wasu na ganin cewa hakan ya bayar da dama ga jam’iyyar PDP ta murmure, ta gyagije, ta kuma samu sukunin mike kafafu har sai ta komo cikin hayyacinta. Akwai alamun da ke nuna cewa wasu tsoffin sabbin Gwamnonin PDP da suka komo cikin APC, suna hada kai da baki da wadanda suka fice daga PDP, suka koma cikin APC bayan kammala zabe don wargaza hadin kai, ko kuma abin da ake kira merger wacce ta wanzar da jam’iyyar APC, kuma wannan na iya yin sanadiyar kai ta kasa. A yanzu dai za a sanya ido ne kan take-taken wasu fitattun ‘ya’yan jam’iyyar APC da suke da tsohuwar alaka da PDP da nufin fahimtar inda bakunansu za su karkata don a san matsayinsu da kuma irin aikace-aikacen da za su iya yi, walau dai don durkusar da jam’iyyar APC ko kuma takura wa Shugaba Muhammadu Buhari da niyyar hana ruwansa gudu. Ta ko ina dai aka kalli wanan al’amarin sai a fahimci cewa akwai sauran rina a kaba. Shi kuma sabon Shugaban Majalisar Dattijai, sai ya dauki matakin yin sulhu da jam’iyarsa, domin kuwa zai bukaci goyon baya da taimakon ‘yan uwansa na Majalisar, ganin cewa a wanan halin da yake ciki yana matukar bukatar jam’iyya fiye da yadda take bukatarsa. Ya kamata ya sani ta inda aka hau ta nan akan sauka, sai ya tuna cewa ja-in-ja shi ke janyo tsinkewa, ya kuma yi taka-tsantsan kada ya tsokalo sama da kara.