Ja-in-ja ke kawo tsinkewa
Akwai abubuwa guda uku da kan dagula al’amura a harkokin siyasar kasar nan a dukkan lokutan da aka waiwaye su wajen gudanar da al’amura. Da farko dai batun zaben shugaban kasa kan jawo yamutsin siyasa da tayar da zaune tsaye; sa’annan kuma akan daddaga hakarkari a dukkan lokacin da aka tashi bayyana sakamakon alkaluman yawan […]
Akwai abubuwa guda uku da kan dagula al’amura a harkokin siyasar kasar nan a dukkan lokutan da aka waiwaye su wajen gudanar da al’amura. Da farko dai batun zaben shugaban kasa kan jawo yamutsin siyasa da tayar da zaune tsaye; sa’annan kuma akan daddaga hakarkari a dukkan lokacin da aka tashi bayyana sakamakon alkaluman yawan jama’a idan an yi kidaya; akan kuma tayar da kura game da batun rabon arzikin kasa tsakanin jihohin da ke jike jagab da arzikin man fetur da wadanda suke busassu, kandas.
Ba wani abu ne ke haddasa haka ba kuwa illa hassadar da wasu kabilu suke yi wa abokan zamansu, abin da ke haddasa bakar gaba bisa tafarkin bambancin addini da bangaranci. Kowace kabila so take ta yi fice ko da kuwa tasirinta a fagen siyasa bai taka kara ya karya ba, kuma kashinta bai yi kwari ba, amma duk da haka nan za ta nemi a ce ba wata sai ita. Dalili kuwa shi ne tsarin mulkin kasar ya tattara dukkan iko da madafunsa ya danka su ga hannun wanda duk ya zama shugaba. Shi zai zamanto mai wuka da nama, sai yadda ya ga dama, ko inda yake so zai yanka, sai kuma wanda yake so zai mikawa. Shi ya sa masu hankoron kai wa ga wannan mukamin sukan dauki gasar shugabancin kasa kan jiki-kan-karfi, ko a mutu, ko a yi rai; sakamakon da zai biyo baya kuma ko oho. Saboda yadda siyasar kabilanci ta yi katutu a kasar nan kowace kablia so take a ce nata ne zai kai ga dankar ragamar mulkin kasar, danginsa kuma za su taimaka masa ta kowace irin hanya don tabbatar da cewa kakarsu za su yanke saka.
Wannan lamari ya dace da yanayin da siyasar kasar nan ke ciki. Batun zaben shugaban kasa ya sha gaban dukkan al’amura, walau na gwamati ne wadanda ya kamata ta yi don sauke nauyin jama’a da ke wuyanta, ko don ciyar da kasa gaba. An tsaya ana ta hatsaniya da hayagaga game da zaben shugaban kasa tun lokacin bai zo ba. ‘Yan Arewa sun ja daga sai mulki ya sake haurowa tudunsu, Shugaba Jonathan da mutanensa sun ce babu wanda ya isa ya yakice su daga nonon da suka fara tsotso alhali sun kai minzalin yaye. Shi ya sa mahukunta suka shantake, suka kasa magance masifu da fitintinu da matsalolin da suka fesowa kasar a jiki kamar kazuwar birni. A yanzu ma ta kai dambarwar neman mulki tsakanin gwamnoni da shugaban kasa, tsakanin ‘ya’yan jam’iyya guda ya kazanta, yana ta dumama kasar ainun, ta kuma tsaya cik, babu wani abin da ke gudana sai maitar da suka amayar na bakin burinsu wanda talakawa suka tabbatar cewa zai kai kasar ya baro a banza.
Wannan shi ne tushen dukkan bala’o’in da suka tayar da kowa tsaye, suka kuma hana siyasar kasar yin armashi, an rasa wanda zai gano dabarun tankwara su don hankalin kowa ya kwanta. A yau idan da Shugaba Jonathan zai hakura, ya ce ba zai sake takara ba, walau don lusarancinsa da rashin sanin makaman mulki, to da ba makawa kurar da guguwar bakin burinsa ta tayar za ta lafa lif. To amma ba zai yi haka ba. Su kuma gwamnonin wasu jihohi da kuma masu adawa da tsayawar tasa ba hakura za su yi ba, naci ke gare su. Al’amarin ya zame gaba kura, baya sayaki ga jama’ar kasar.
Dangane da haka ne ake dambarwa kan matsayin gwamnoni game da shugabancin jam’iyya a jihohinsu. Shugaban kasa da kuma mahukuntar jam’iyya na son kwace wannan ikon da gwamnoni ke da shi, su danka ragamar jam’iyyar kacokan ga shugaban kasa domin a karkade hannayensu daga samar da wakilai (delegates) da za su halarci babban taron jam’iyya don fitar da dan takarar shugabancin kasa. Su kuma gwamnoni suna tunkaho da kungiyarsu don tadiye Shugaba Jonathan, wacce a yanzu haka ta kasance tamkar mushen gizaka: ga shi dai ta mace amma har yanzu tana ba yaro tsoro.
Yanzu abin da ya rage sai a sanya ido, a jira yadda sharudda goma da wasu gwamnonin jam’iyyar PDP biyar suka gindaya kafin a dinke barakar da hadamar mulki ta wanzar, ko za su taimaka a samo zaren dinke waccan barakar? Cikin wadannan sharuddan akwai batun rashin takarar Shugaba Jonathan da canja shugabancin jam’iyyar don kada a hana ruwan gwamnonin gudu a jihohi da kuma amincewa da shugabanci Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi na kungiyarsu ta gwamnoni. Masu lura da al’amura na ganin cewa an rigaya an wuce wannan wuri tuni, amma gwamnoni na so a ci gaba da ja-in-ja, kuma hakan na iya jawo tsinkewar ragamar jam’iyyar daga hannun shugabanninta.