Jabun wakilin rediyon BBC ya shiga hannu a Nasarawa

Wani matashi da yake gabatar da kansa a matsayin wakilin sashin Hausa na gidan rediyon BBC Landan a Arewa ta Tsakiya ya shiga hannun ’yan sanda a Jihar Nasarawa. Daraktan Cibiyar Lafiya ta tarayya (FMC) da ke Keffi a jihar, Dokta Joshua Giyan ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin mai suna, Nura […]

Jabun wakilin rediyon BBC ya shiga hannu a Nasarawa
Jabun wakilin rediyon BBC ya shiga hannu a Nasarawa

Wani matashi da yake gabatar da kansa a matsayin wakilin sashin Hausa na gidan rediyon BBC Landan a Arewa ta Tsakiya ya shiga hannun ’yan sanda a Jihar Nasarawa.
Daraktan Cibiyar Lafiya ta tarayya (FMC) da ke Keffi a jihar, Dokta Joshua Giyan ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin mai suna, Nura Mohammed ya same shi a ofishinsa cewa yana so ya tattauna da shi game da wasu batuttuwa da suka shafi cin hanci da rashawa da ake zargin mahukuntan cibiyar.
Daraktan ya ce sai suka shirya cewa Nura Mohammed ya dawo washegari don su tattauna. Ya ce kafin Nura ya dawo ne sai ya bincika a wurin wadansu ’yan jarida inda ya gano cewa Nura ba wakilin BBC ba ne, kuma ya gano gidan rediyon bai ma da wakili a jihar.
Ya ce shigowar Nura Mohammed ke da wuya sai ya umarci jami’an tsaron cibiyar su tsare shi don mika shi ga ’yan sanda.
Dokta Giyan ya bukaci ’yan sanda da kungiyar ’yan jarida a jihar su tabbatar an hukunta wanda ake zargin don ya kasance darasi ga ire-irensa.
Ya musanta zargin cin hanci da rashawa da karancin kwararrun likitoci a cibiyar inda ya ce wannan zargi ne daga wadanda ba sa son ci gaban cibiyar da kasar nan.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Nura Mohammed ya ce “Ni ma’aikacin gidan rediyon jihar nan ne kuma ni wakilin rediyon BBC Hausa ne a shiyyar Arewa ta Tsakiya. Na tafi wajen daraktan cibiyar ne don in samo bayyanai daga wurinsa game da zargin cin hanci da rashawa da wasu ke yi wa mahukuntan cibiyar.
Janar Manajan gidan rediyon jihar (NBS), Alhaji Yusuf Musa ya bayyana wa Aminiya cewa kodayake Nura Mohammed ya taba aiki da gidan rediyon, amma an dade da sallamarsa sakamakon munanan dabi’unsa. Wani babban jami’in BBC da ke Abuja, Muhammad Kabir Muhammad ya ce Nura Mohammed ba wakilin BBC ba ne.