Jabun wayoyi: Ingantar wutar lantarki na iya jawo yawan gobara a gidaje
Gwamnati tana ta aiki ba kama hannun yaro domin tabbatar da an samar da wadatacciyar wutar lantarki a kasar nan. Gwamnatin Tarayya ta kashe fiye da Naira tiriliyan biyu da rabi kan wutar lantarki daga shekarar 2009 zuwa 2014.An ruwaito Dokta Aiku Abubakar Mataimakin Manajan Daraktan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), yana cewa, […]
Gwamnati tana ta aiki ba kama hannun yaro domin tabbatar da an samar da wadatacciyar wutar lantarki a kasar nan. Gwamnatin Tarayya ta kashe fiye da Naira tiriliyan biyu da rabi kan wutar lantarki daga shekarar 2009 zuwa 2014.
An ruwaito Dokta Aiku Abubakar Mataimakin Manajan Daraktan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), yana cewa, kimanin Naira biliyan 15 kasar nan take nema domin ta samar da wutar lantarki mai karfin megawatt dubu takwas zuwa karshen bana.
Sai dai a cewar Onogwu Isah Muhammed: “Hujjoji sun nuna idan ana son a cimma wannan bukata ta jama’a, to Najeriya za ta fada cikin wata babbar matsala, domin yiwuwar rushewar gidaje da aukuwar gobara za su kasance abin da ke aukuwa a kusan kullum.”
Ya ce a ksauwar gine-gine ta Najeriya ta yau, wayoyin da suke da girman milimita 2.5 ba za su iya daukar nauyin wuta milimita 1.5 ba. Wani gwaji da aka gudanar a takaice ya gano cewa kasar nan tana gabar fadawa cikin wani bala’i matukar Kamfanin Lantarki na kasa (PHCN) ya rika samar da wutar lantarki a kai-a kai ga gidajenmu.
Onogwu ya ce: “Na yi amfani da samfurin wayoyi uku domin gudanar da gwaje-gwajen bayan dutsen gugana da soket sun kone. Soket din lantarkina (na Royal kuest na Ingila) mai daukar karfi wuta 220-240b, nan take wayar ta kone ta lalata soke din. Na sake sayo wani soket karfinsu daya da wancan, amma a wannan karo da dutsen gugar da bai kai wancan ba, sai dai wayar ba ta fashe ba, sai ta rika narkewa kamar kyandir. Wannan ya nuna cewa wadanda ake cewa sun kai 220-240b, a zahiri ba su wuce karfin 120b ba.”
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas kadai ta ce, mutum 79 suka mutu a sassan jihar sakamakon hadarin gobara a jihar a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban bara.
Kakakin Hukumar Mista Amodu Shakiru ya bayyana haka, ind ya ce: “Daga hadarin gobara 1, 638 da aka samu a jihar dukiya ta Naira biliyan 16 da miliyan 380 aka yi asara a hadarurrukan tare kuma da rugujewar gidaje 11.”
Abin da Onogwu ya hadu das hi yana faruwa a gidaje da dama a kasar nan bias dalilai irin wadancan. Kuma duk da cewa kebul-kebul da wayoyin da aka kera a Najeriya suna daga cikin mafiya kyau wajen inganci da karko, masu sana’anta su suna fuskantar matsaloli da dama.
Binciken da jaridar Aminiya ta gudanar ya gano cewa wayoyin da aka sana’anta a Najeriya kamar samfurin na Kamfanin Coleman Cables and Wires, sun samu takardar shaidar inganci ta Hukumar Kula da Inagancin Kaya ta Duniya (ISO), wanda hakan ya ba shi dammar da zai iya sarrafa wayoyinsa ya kai ko’ina a duniya, amma duk da haka yana fuskantar kalubale daga wayoyi masu araha da rashin inganci da suke fitowa daga kasashen Asiya. Kayayyaki marasa ingaci suna jawo asara ga kamfanonin wayoyin lantarki ta kimanin Dala biliyan 60 a kowace shekara a duniya.
Injiniya Emmanuel Adugbo, wani injiniyan lantarki ya ce: “Idan akwai wani kayan da aka kera a Najeriya da masu saye za su aminta das hi, to wayoyin wutar lantarki da kebul-kebul ne suka cancanci hakan. Masana’antu da dama sun kintsa don yin gasa a wannan bangare. Da dama sun samu lambobin yabo a banagren sana’anta wayoyin lantarki da wayoyin tarho, amma da kyar suke dorewa saboda gasar da suke fama da ita daga wayoyin lantarki masu araha da rashin inganci da ake shigowa da su daga waje.”
Injiniya Emmanuel ya nanata cewa sakamakon karancin karfe in aka kwatanta da sinadari ko gorar ruwa za a ga cewa a kimiyyance bai dace a yi amfani da dutsen guga irin wannan ba.
“Saboda irin wutar da karfe ke ja, dusten guga kan yi zafi sosai fiye da ace an yi sanya masa sinadari ko gorar ruwa. Idan haka ta faru sakamakon da za a samu shi ne saurin daukar zafi da yiwuwar fashewar hanyar wutar lantarkin ko na’urar da ka iya jawo gobara da asarar rayuka da dukiya a karshe a jawo wa kasa asara a fagen tattalin arziki,” inji shi.
Emmanuel ya kara da cewa, ba a amfani da karfe a matsayin mai sadar da wutar lantarki a duk kasashen da suka ci gaba, saboda yadda yake yake saurin jawo wuta da kuma hadarin da yake haifarwa, kuma a lokacin da karfin wutar lantarki ya bi ta cikin karfe yakan hanzarta daukar zafi tare da jawo barna.
Ya ce raguwar ingancin da ake samu a wayoyin lantarki a wasu lokuta yakan kai murabba’in mita 2.5 zuwa 7.73, wanda hakan ke sanya su yin zafi su gaza daukar wutar da a karshe ke iya jawo barkewar gobara.
Aminiya ta gano cewa, masu shigo da kayayyakin suna samun nasarar cimma muguwar manufarsu ce saboda rashin katabus daga cibiyoyi da hukumomin tabbatar da ingancin kayayyaki da rashin dokoki da rashin ingancin aiwatar da tsare-tsare wadanda suke haifar da tababa kan ikon Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON) na ta taka birki ga shigo da jabun kayayyaki da marasa inganci zuwa kasar nan.
Darakta Janar na kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu ta Legas (LCCI), Mista Muda Yusuf ya ce kwararowar wayoyin lantarki marasa inganci zuwa cikin kasar nan na faruwa ne saboda rashin bin doka da ka’idoji da kuma gazawar dokokin kasar nan.
Ya ce: “Mun gano ana samun yawan aukuwar gobara a ’yan shekarun nan, inda take jawo asarar dukiya ta miliyoyi ko biliyoyin Naira, bincike kana bin da ke kawo wannan hadari ya dora laifi kan amfani da kayayyakin gini marasa inganci musamman wayoyin lantarki.”
Abin tambaya a yanzu shi ne yaya za ka gane waya mai kyau? Injiniya Emmanuel ya ce: “Ba abu ne mai sauki a gane gangariyar wayar lantaki ba, magani shi ne ka sayi wayar lantarki daga dillalan wayoyin lantarki da hukuma ta amince da su.”
Ya ba da shawarar cewa, kafin a duba wayoyin lantarki masu saye su binciko na wane kamfani ne da kuma ingancinta. Idan wayar lantarkin ba ta da inganci, to kada a tsammaci kariya ko kargo daga gare ta.
A duk lokacin da za ka yi amfani da wayoyin lantarki a gidanka, ka zabi wayoyin da aka (sana’anta a Najeriya) domin sun fi karko da inganci da kuma bayar da kariya.
Injiniya Emmanuel ya kara bayar da shawarar cewa: “Yana da matukar muhimmanci a duba yanayin da wayoyin lantarki suke ciki a kai-a kai. Kuma a yayin duba wayoyin a rika duba duk inda suka karye ko suka katse, karamar katsewa ko karyewa na iya jawo hadarin wuta. Kuma rashin canja irin wadannan wayoyi na iya jawo matsalar da ka iya kawo babbar gobara.”
kwararren ya ce akwai bukatar a rika gano inda aka tankwara ko aka hada wayoyin lantarki ba bisa ka’ida ba don a hanzarta gyara su ta yadda daga baya ba za su jawo matsala ba.
Mista Gracious Omatseye Shugaban Cibiyar Injiniyoyin Lantarki da Kaya masu Amfani da Wutar Lantarki ta Najeriya (NIEE), ba a bar shi a baya ba, wajen nuna damuwarsa kan yawaitar aukuwar gobara a kasar nan. Ya ce kasha 90 cikin 100 na gidaje a Najeriya ba su bin ingantacciyar hanya sanya wutar lantarki wanda hakan ne ke kawo yawaitar hadarin gobara.
Omatseye ya kara da cewa, yin amfani da wayoyin lantarki masu kyau da bin tsarin da ya dace da sauransu zai rage yawan tashin gobarar.
Misis Yemisi Bode-Thorpe Janar Manajar Kamfanin Coleman Cables and Wires lokacin da take nuna damuwarta kan wayoyin lantarki marasa inganci ta ce ayyukan wadanda ta kira ‘marasa kishin kasa’ a cikin ’yan kasuwar da suke zuwa China da Indiya wadanda ba ma suna sayo jabun wayoyi kadai ba ne, har ma sukan bukaci a rage karfi ko yawan sinadarin da ke cikin waya da kebul, wanda shi ne ke jawo gobara a ofisoshi da gidaje.
Ta ce: “Don haka mun damu kan yadda manyan dillalai a Kasuwar Alaba da ke Legas ke yin jabun kayayyakinmu, kuma muna so jami’an tsaro kan wannan zagon kasa.”
Daraktan Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON) da ya gabata, Dokta Joseph Odumodu ya fadi a shekarar 2015 cewa domin katse rarraba wayoyin lantarki marasa inganci Hukumar SON ta kwace wayoyin lantarki marasa inganci na Naira miliyan 450 a Kasuwar Alaba bayan farmakin farko da ta ga wasu tireloli tara shake da wayoyin lantarki marasa inganci da kudinsu ya kai Naira miliyan 200.
Yayin da galibin wayoyin lantarkin ke fitowa daga Asiya musamman China, a cewar kungiyar Yaki da Jabun Kayayyaki ta Duniya (IACC), ta kiyasta ana asarar kudin haraji day a kai Dala biiliyan 125 da kuma wasu karin kudin inganta rayuwa da ake kashew3a a kasashe masu tasowa kadai, yayin da ake rasa gurabun aiki miliyan biyu da rabi.
Odumodu ya ce: “Wannan batu na kayayyaki marasa inganci matsala ce ta Najeriya bat a Hukumar SON kadai ba, ta shafi kowa. Babban abin takaici idan ka je wurin kungiyar masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) amma ka gano kasha 60 cikin 100 na kamfanoninta sun rufe saboda wannan matsala. Wadanda suke shigowa da wadannan kayayyaki marasa inganci suna jawo rashin aikin yi da rashin zaman lafiya a kasa, wadanda a kaikaice suke dada iza wutar ta’addanci. Sai mutane sun dada zage dantse suna Magana a kan haka ne za a tsabtace mana Najeriya.”
Wani kwararren masanin gine-gine Mista bincent Benard ya ce: “Gwamnati ba ta yin abi da ya kamata wajen fadakar da jama’a kan hadarin amfani da jabun wayoyin lantarki a gine-ginensu. Wajibi ne mutane su fahimci illar yin amfani da jabun wayoyin lantarki da kuma alherin da za a samu wajen sayen wayoyin lantarki mafiya inganci da aka sana’anta a Najeriya, arahar wayar lantarki za ta zama ta banza idan ka rasa ranka ko na wani danginka ko dukiyarka. Don haka idan aka fahimtar da mutane su fahimci haka, an samu nasarar wannan yaki da kashi 50 cikin 100, saboda za a daina sayen jabun kayayyakin da ake shigowa da su, saura kuma a samar da sanya ido a kan iyakokinmu da masu sayar da kayayyakin wadanda suke hada baki da wadannan ’yan sumoga.”