Jack Sparrow: Dalilin cire Johnny Depp daga fim din ‘Pirates of the Caribbean’
Shari’ar zargin cin zarafin tsohuwar matarsa ta sa kamfanin Disney cire Johnny Depp daga fim din ‘Pirates of the Caribbean’
An maye gurbin jarumin da ke fitowa a matsayin Captain Jack Sparrow a shahararren fim din ‘Pirates of the Caribbean’, wato Johnny Depp, kamar yadda ya bayyana da kansa.
Shi ma wani tsohon manajan Johnny Depp a masana’antar fim ta Hollywood, Christian Carino, ya sanar da hakan a gaban kotun da ke sauraron shari’ar tauraron fim din da tsohuwar matarsa, Amber Heard.
- Sam ba da Nafisa nake maganar tarbiyya ba – Sarkin Waka
- A Kannywood ne zaka ga ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su – Sarkin Waka
Da yake magana kan cire Johnny Depp daga matsayin Jack Sparrow, Christian Carino, ya shaida wa kotu cewa, “Ra’ayina shi ne hakan na da alaka da zargin da Amber ta yi mishi.”
Christian Carino wanda yanzu ma’aikacin kamfanin fim na Creative Arts Agency ne, ya bayyana haka ne a shaidar da ya bayar ta bidiyo a gaban kotun da ke sauraron shari’ar tsoffin ma’auratan.
Kamfanin Disney ya dakatar da Johnny Depp daga fitowa a matsayin Jack Sparrow a fim din Pirates of the Caribbean ne bayan Ambar Heard ta yi karar shi kan zargin duka da kuma cin zarafinta a baya.
A shari’ar, Amber na neman diyyar Dala miliyan 100 daga Johny Depp kan cin zarafi da kuma dukan da take ikirarin ya yi mata a lokacin da take matsayin matarsa.
Ta shigar da kara ne bayan ya maka ta a kotu yana neman ta biya shi Dala miliyan 50 kan zargin bata mishi suna a fakaice, lamarin da ake zargin ya kai ga cire shi a shaharren fim din Pirates of the Caribbean.
Majiyoyi a Hollywood sun ce Disney sun cire Johnny Depp daga matsayin Jack Sparrow, ko da yake kawo yanzu dai kamfanin, wanda ke shirya fim din na Pirates of the Caribbean bai ce komai ba.
Da farko Johnny ne ya yi karar Amber, jaruma a Hollywood, saboda wata makalarta da aka wallafa a jaridar The Washington Post a watan Disamban 2018.
A cikin makalar, tsohuwar matar tasa mai shekara 36 ta bayyana cewa ita “shahararriyar mutum ce da ke zama a matsayin misali na wadda ake duka da cin zarafi.”
Amber dai ba ta ambaci sunansa ba, amma ya maka ta a kotu yana neman diyyar Dala miliyan 50, da cewa makalar tana nuni zuwa gare shi a fakaice cewa shi mai cin zarafi ne.
Daga baya ita kuma ta shigar da kara tana neman diyyar Dala miliyan 100, cewa ya “sha duka da cin zarafin ta,” a lokacin da suke aure.
Ya shigar da karar a Amurka ne, bayan ya sha kaye a shari’ar da ya maka Jaridar The Sun ta kasar Birtanyya, kan kiran shi da ‘Mai dukan mace.”
Carino wanda tsohon manajan tsoffin ma’auratan ne, ya bayyana cewa kamfanin Disney bai fito fili ya fada cewa zargin cin zarafin ne ya sa ya cire jarumin matsain Jack Sparrow a fim din Pirates of the Caribbean ba, amma “an fahimci hakan.”
Tun da farko da yake rantsuwa a gaban kotun, Johnny Deppy ya dora laifin cire shi daga matsayin Captain Jack Sparrow a fim din Pirates a kan zarge-zargen da Amber Heard ta yi mishi.
Da yake ba da shaida a makon jiya, Depp ya ce zarge-zargen da ake yi masa na cewa “mai shaye-shayen hodar iblis da ke dukan mata” ne ya janyo masa “asarar komai.”
Ya musanta cewa ya taba cin zarafin Heard, hasali ma ita ce ta kasance mai yawan tashin hankali.
Depp, wanda ya lashe kyautar Oscar sau uku, da Heard sun hadu ne a 2009 a wurin daukar fim din “The Rum Diary”.
Sun yi aure a watan Fabrairun 2015 amma suka rabu bayan shekara biyu.