Jackie Chan ya yi magana da Hausa

Fitaccen jarumin fim din nan dan kasar China, Jackie Chan ya yi magana da Hausa da Ingilishin Pidgin, da Yarbanci da kuma Ibo, a matsayin gayyatar masoyansa don su je kallon sabon fim dinsa mai suna “Dragon Blade” wanda za a sake shi a yau Juma’a a gidajen siliman da ke kasashen Najeriya da Ghana.Fim […]

Jackie Chan ya yi magana da Hausa
Jackie Chan ya yi magana da Hausa

Fitaccen jarumin fim din nan dan kasar China, Jackie Chan ya yi magana da Hausa da Ingilishin Pidgin, da Yarbanci da kuma Ibo, a matsayin gayyatar masoyansa don su je kallon sabon fim dinsa mai suna “Dragon Blade” wanda za a sake shi a yau Juma’a a gidajen siliman da ke kasashen Najeriya da Ghana.
Fim din Dragon Blade ya samu gagarumar kasuwa a kasar China kuma yanzu za a gwada shi a Najeriya da Ghana da sauran nahiyoyi bisa fatar ya samu karbuwa.
Fim din yana da Daniel Lee a matsayin darakta yayin da jarumansa suka hada da Jackie Chan da John Cusack (Zakaran Golden Globe) da Adrien Brody (Zakaran Academy Award) da Choi Si Won da kuma diao Yang. Kuma kamfanin FilmOne Production and Distribution Company ne yake rarraba shi a duniya.