Jackie Lindsey: Matar da ta tsani wutar lantarki
Jackie Lindsey wata mata mai kimanin shekara 50 da haihuwa, wadda take zaune a kasar Birtaniya. Sai dai ita ta fita daban da sauran mutane saboda yadda jikinta ya tsani wutar lantarki da kuma na’urorin da ke amfani da ita ciki har da wayar salula, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ranar Juma’ar da ta […]
Jackie Lindsey wata mata mai kimanin shekara 50 da haihuwa, wadda take zaune a kasar Birtaniya. Sai dai ita ta fita daban da sauran mutane saboda yadda jikinta ya tsani wutar lantarki da kuma na’urorin da ke amfani da ita ciki har da wayar salula, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ranar Juma’ar da ta gabata ta ruwaito.
Hakazalika, tana amfani ne da kendir wajen samar da haske a gidanta idan dare ya yi. Kodayake, tana amfani da na’urar gas ne wajen girki da dumama dakinta a lokacin sanyi. Jaridar ta ce wannan lalurar da Jackie ke fama da ita ba a saba ganin irinta ba a kasar Birtaniya, amma an taba samun ta a kasar Sweden.
A wani lokaci a baya, sai da Jackie ta sayar da tsohon gidan da take ciki saboda yadda ta ce “wutar lantarkin gidan makwabcinta yana cutar da ita.” Hakan ya sa a yanzu tana zaune ne wani gida da ke nesa da gari.
Jackie ta ce ba ta iya tsaya wa kusa da duk wani wanda yake amfani da wayar lalula domin tsoron kada na’urar ta cutar da ita. Har ila yau, kowane lokaci idan za ta fita waje, ta kan sayan wasu tufafi domin kariya daga hasken rana.
Ta ce kafin ta fahimci lalurar, sai da ta kwashe shekara uku tana nazari a kanta, inda daga nan ta fahimci cewa alamomin sun yi daidai da na mai cutar da ake kira Elecromagnetic Hypersentibity a harshen Inglishi. “Yawancin wadanda suke fama da irin wannan cutar suna rabuwa da danginsu da ’yan uwa da abokan arziki. Domin ba lalle ba ne su fahimci lalurar yadda take a zahiri, galibin jama’a suna iya ganin kamar matsala ce ta tabun hankali,” inji ta.