Jadawali: Makomar kungiyoyin da suka rage a Gasar Zakarun Turai

Wasan karshe na Gasar Zakarun Turai za a fafata shi ne a ranar 10 ga watan Yuni.

Jadawali: Makomar kungiyoyin da suka rage a Gasar Zakarun Turai

Dan wasan Real Madrid Karim Benzema kenan daga hagu, tare da dan wasan Liverpool Trent Alexander-Arnold a wasan karshe na gasar Zakarun Turai, ranar 28 ga watan Mayun 2022.

A ranar Juma’ar wannan mako ne dai za a fitar da jadawalin dab da na kusa da na karshe a gasar.

Chelsea, Bayern Munich, AC Milan da Benfica sun samu tabbacin kai wa gurbin ’yan takwas a matakin daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Manchester City, Liverpool da Real Madrid mai rike da kambun gasar kuwa har yanzu suna fatan zuwa zagayen ’yan takwas din.

Chelsea ce kadai a kungiyoyin Ingila da ta kai zagayen na kwata final bayan ta doke Borussia Dortmund da ci 2-1 a zagayen na ’yan 16.

Manchester City da Liverpool su ne sauran kungiyoyin Firimiyar Ingila da har yanzu za su iya kaiwa matakin ko kuma akasin haka, inda kungiyoyin biyu suka buga wasansu na biyu a wannan makon.

A wannan Talatar ce City za ta kara da RB Leipzig a filin wasa na Etihad bayan da kungiyar karkashin Pep Guardiola ta tashi kunnen doki 1-1 a Jamus a wasan farko.

Ita kuwa Liverpool, za ta fuskanci wani gagarumin aiki ne a yunkurinta na kawar da rashin nasarar da tayi a hannun Real Madrid da ci 5-2 a zagayen farko, inda za a yi wasa na biyu ranar Laraba a Bernabeu.

Dama Tottenham tuni aka yi waje da ita, bayan kayen da ta sha a zagayen farko a hannun AC Milan da ci 1-0 a zagayen farko, inda a zagaye na biyu kuma suka tashi a wasan nasu babu ci.

Bayern Munich da Benfica su ma sun tsallaka zuwa matakin na gaba, inda Inter Milan ko Porto da Eintracht Frankfurt ko Napoli ke fatan haduwa da su a zagayen na ‘yan takwas ko kuma dab da na kusa da na karshe.

Jadawalin dab da na kusa da na karshe

Za a fitar da jadawalin kwata final da wasan kusa da na karshe a ranar 17 ga watan Maris, a birnin Nyon da ke Switzerland, wato shelkwatar UEFA.

Za a buga zagayen farko na kwata final ranar Talata, da Laraba, wato 11 da 12 ga Afrilu, sannan zagaye na biyu kuma, za a fafata ne a ranar 18 da 19 ga watan na Afrilu.

Yaushe ne za a buga wasan kusa da na karshe?

Zagayen farko na wasan kusa da na karshe za a yi shi ne ranar 9 da 10, ga watan Mayu, sai kuma ranar 16 da 17 ga watan Mayu da za a buga zagaye na biyu.

Ranar da za a buga wasan karshe

Wasan karshe na Gasar Zakarun Turai za a fafata shi ne a ranar 10 ga watan Yuni, a filin wasa na Ataturk Olympic da ke birnin Istanbul, na kasar Turkiyya.