Jadawalin Gasar AFCON 2023 da za a fafata baɗi a Ivory Coast

Rabon da Najeriya ta samun nasarar lashe Gasar AFCON tun wadda ta yi a shekarar 2013.

Jadawalin Gasar AFCON 2023 da za a fafata baɗi a Ivory Coast

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu gurbi a rukuni daya tare da mai masaukin baƙin Gasar Kofin Afirka AFCON ta 2023, Ivory Coast.

A gasar wadda za a fafata a Janairun baɗi, Najeriya, Guinea Bissau, Equaitorial Guinea da kuma Ivory Coast (Cote d’Ivoire) sun tsinci kansu a rukuni na farko wato Group A.

An dai gudanar da bikin fitar da jawadalin ne a daren jiya na Alhamis a Pars de Expositions da ke birnin Abidjan.

Tsohon tauraron Ivory Coast da ya taka leda da Chelsea kuma wanda ya taba lashe gwarzon shekara na Afirka har sau 2, Didier Drogba da kuma tauraron Najeriya, Jon Mikel Obi da ya lashe kofin AFCON a 2013 na sahun wadanda suka yi aikin rarraba kasashen na Afirka zuwa rukunnai don tunkarar wasan na watan Janairu.

Mai masaukin baƙin, Ivory Coast, wadda ta lashe Gasar AFCON a shekarar 1992 da kuma 2015, za ta bude gasar a wasan da za ta kece-raini da Guinea Bissau ranar 13 ga watan Janairu.

In other draw highlights, defending champions Senegal were pitted against Cameroon, while record winners Egypt will renew hostilities with Ghana.

Masar mai faƙon ganin ta lashe gasar karo na takwas a tarihi, za ta yi gumurzu da Ghana da Cape Verde da Mozambique a rukuni a guda.

Morocco wadda ta kai wasan gab da na karshe a Gasar Kofin Duniya bara a Qatar, wadda kuma za ta karbi baƙuncin Gasar AFCON a 2025, a na ta rukunin za ta hadu da kasashen Congo da Zambia da kuma Tanzania.

A jawabinsa, bayan fitar da jadawalin, dan wasan gaba na tawagar Moroccon da aka fi sani da Atlas Lions, Achraf Hakimi wanda shi ma ke sahun ‘yan wasan da suka yi aikin rarraba kasashen, ya ce za su yi iyakar kokarinsu, kwatankwacin abin da suka yi a Gasar Kofin Duniya.

Za a fafata wasannin gasar ce a filayen wasa shida a fadin kasar ta Ivory Coast, ciki har da sabbin filayen wasan da aka gina a Abidjan da Korhogo da San Pedro.

Ga dai yadda jadawalin ya ke:

Rukunin A na kunshe da kasashen Ivory Coast da Najeriya sai Equatorial Guinea da Guinea-Bissau.

Rukunin B akwai kasashen Masar da Ghana da Cape Verde da kuma Mozambique.

Rukunin C akwai kasashen Senegal da Cameroon da kuma Guinea baya ga Gambia.

Rukunin D akwai Algeria da Burkina Faso sai kuma Mauritania da Angola.

Rukunin E na kunshe da kasashen Tunisia da Mali da Afrika ta kudu sannan Namibia.

Rukunin F kuma na karshe na dauke da kasashen Morocco sai jamhuriyyar Demokradiyyar Congo kana Zambia da Tanzania.

Ana iya tuna cewa, Najeriya wadda ta lashe Gasar AFCON karo uku a tarihi, rabonta da samun nasara tun a gasar da aka fafata a 2013.

Haka kuma, a watan Afrilun 1994 ne tawagar kwallon kafar Najeriya ta kai matsayi na biyar jerin kasashen duniya mafi bajinta da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta fitar.

Wannan dai ita ce mafi bajinta da aka ta samu daga wata tawagar kwallon kafa a duk nahiyyar Afirka.