Jadawalin zagayen ’yan 16 na Gasar AFCON

Kasashe 12 sun samu cancantar tsallakawa matakin wasannin sili daya kwala.

Jadawalin zagayen ’yan 16 na Gasar AFCON

Bayan ana tashi wasan Burkina Faso da Algeria

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyyar Afirka CAF ta fitar da jadawalin kasashe 16 da za su fafata a mataki na gaba a Gasar Kofin Nahiyyar Afirka AFCON da ke gudana a Ivory Coast.

An fitar da jadawalin ne bayan kammala wasannin rukuni na gasar AFCON, inda aka tsamo kasashe 12 daga cikin 24 da suka samu cancantar tsallakawa matakin wasannin sili daya kwala ta hanyar yawan makinsu, bayan kammala wasannin rukunin a matsayin ko dai na farko ko kuma na biyu.

Sauran tawagar kasashe 4 na daban kuma an zabe su ne domin daidaita lissafin ya zamana an samu kasashe 16 da za su fafata a matakin na gaba wato zagayen ’yan 16.

Kasashen da aka zaba galibi sun kammala wasannin rukunin ne a matsayin na 3, amma sun tabuka wani abu, inda za su ribaci tsarin nan na wadanda ake kira best losers.

Jerin kasashen da za su fafata a matakin gasar na ‘yan 16 sun kunshi Equatorial Guinea da Najeriya da kuma Ivory Coast mai masaukin baki dukkaninsu daga rukunin A.

Sai rukunin B wanda kasashen Cape Verde da Masar suka fito daga cikinsa, mai rike da kambu Senegal wadda ta kammala da maki mafi yawa a wasannin na rukuni daga rukunin C da kuma Kamaru da Guinea duk dai a rukunin.

A rukunin D akwai Angola da Burkina Faso da kuma Mauritania, sai rukunin E da kasashen Mali, Afrika ta kudu da Namibia, kana rukunin F wanda kasashen Morocco da Congo suka iya fitowa.

Jadawalin wasannin na matakin ‘yan 16 ya nuna yadda za a yi karon-batta tsakanin kasashen da suka fito kamar haka:

Angola da Namibia

Najeriya da Kamaru

Guinea da Equatorial Guinea

Masar da Congo

Cape Verde da Mauritania

Senegal da Ivory Coast

Mali da Burkina Faso

Morocco da Afrika ta Kudu