Jaddawalin zaben 2015 ba shi ne abin kallo ba

A makon da ya gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta fitar da jaddawalin zaben 2015. Tun daga lokacin ne masana da sauran al’umma suka yi ta tsokaci daban-daban a kansa. Hatta Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bara game da shi, inda ya yi zargin cewa an shirya shi ne ta yadda […]

Jaddawalin zaben 2015 ba shi ne abin kallo ba

A makon da ya gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta fitar da jaddawalin zaben 2015. Tun daga lokacin ne masana da sauran al’umma suka yi ta tsokaci daban-daban a kansa. Hatta Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bara game da shi, inda ya yi zargin cewa an shirya shi ne ta yadda zai taimaki Shugaban kasa Goodluck Jonathan domin ya samu nasarar zarcewa a mulki a 2015. Shi kuwa Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka (08165270879), dogon sharhi ya aiko mana a kan al’amarin, ga abin da yake cewa:
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a Najeriya na cikin mawuyacin hali ba don komai ba sai saboda yadda ta rasa yarda da aminci a tsakanin ’yan Najeriya. Yau har ta kai shugabanta, Farfesa Jega bai iya halartar daurin aure ko tarukan jama’a a wasu sassa na Najeriya. Wannan rashin aminci da Hukumar Zaben Najeriya ke fama da shi, ba karamar cikas zai mata ga ikirarin da shugabanta Farfesa Attahiru Jega ke yi na gudanar da sahihin zabe a 2015 ba.
Wannan matsala ta rashin yarda, da yawa wasu talakawan Najeriya ke ma wannan hukuma ya sanya lokacin da makon da ya wuce ta fito da jaddawalin zabe, kungiyar Dattawan Arewa ta fito fili ta ce ita ba ta yarda a yi zabe sau biyu ba, don haka suka ba da shawarar a hada dukkanin zabukan tun daga na Shugaban kasa zuwa na ’yan majalisun jihohi, a yi su duk rana daya.
Ni a ra’ayina, gudanar da zabe rana daya ba shi ne mafita ba, domin mai son abinka ya fi ka dubara. Kuma ma wani hanzari ba gudu ba shi ne, jaddawalin zabe bai cikin abubuwan da ke sa a samu ingantaccen zabe, don haka yanzu bari mu fara nazarin abubuwan da ke sa a samu ingantaccen zabe:
Masana kimiyyar siyasa kamar su Dokta Abubakar Saddik Muhammad na Tsangayar Kimiyyar Siyasa da ke Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a cikin kasidarsa mai taken ‘Shin Zaben 12 Ga Watan Yuni Amintacce Ne?’ ya lissafta abubuwan da ke tabbatar da zabe ya zama ingantacce ko akasin haka. Na farko, jam’iyyun siyasa: Wadanda jama’a ne da kansu suka kafa su kuma wadannan jam’iyyu an kafa su ne bisa akida da manufofi wadanda aka tallata wa jama’a suka kuma saya ko nuna amincewa da su.
Na biyu, yadda wadannan jam’iyyu suka gudanar da zabukansu na fidda gwani: Shin jama’a ne suka yi zaben ko kuwa wasu daban ne suka dora wa jama’a ’yan takara?
Na Uku, yadda su kansu jam’iyyun suka gudanar da kamfen dinsu cikin aminci da lumana. Sai shi kansa yadda zaben ya gudana a ranar zabe.
Abu na karshe shi ne, yadda kotunan sauraren kararrakin zabe suka gudanar da aikinsu ba tare da son rai ba.
Wadannan su ne abubuwan da ya kamata mu talakawan Najeriya mu duba, mu tabbatar akwai su a siyasar Najeriya, idan har da gaske muna son sahihin zabe a Najeriya. Shi kansa Farfesa Attahiru Muhammad Jega ya dace a ce ya yi murabus saboda mutane da yawa ba su amince da shi ba. To sai dai yadda lokaci ya kure, yana da matukar wahala hakan ta tabbata. Don haka sai mu yi abin da ke iya yiwuwa, maimakon mu ci gaba da bata lokacinmu a kan batun jaddawalin zabe, wanda bai cikin abubuwan da bincike ya nuna suna taimakawa a samu sahihin zabe ba.
Mu kuma talakawa, dole mu daina sayar da kuri’unmu inda ake ba mu sabulu da taliyar indomi ko fallen zane. Mu daina bangar siyasa da tada hargitsi. Wadannan matsalolin da muka zayyana, su suka kamata ’yan Najeriya su maida hankali a kansu, ba wai jaddawalin zabe ba.
***

Hidindimun Gizagawa na wannan makon:
Gizagawan Jihar Kaduna za su gudanar da taro a jibi Lahadi, a Kawo Kaduna, da misalin karfe 11:00 na safe. Domin karin bayani, sai a tuntubi PRO a 08036003631.
A labarin farin ciki kuwa, Bagizage Hafiz Ibrahim Dambam (GZG209BAU) 08106695097, za a daura aurensa a gobe Asabar da karfe 11:00 na safe, a gidan Alhaji Babayo danfanta, tsohuwar kasuwar Dambam.
Shi ma Yusuf Musa (08039119552), wan Sunusi CBN, za a daura nasa auren a gobe Asabar, a Unguwar Kobi, Bauchi.
A labarin jajantawa kuwa, mahaifiyar Bagizage, Hussaini Nakura Daura (07034900185) ta rasu.
Shi ma Auwalu Kabiru Durumin Zungura Kano, 08096224490, Allahh Ya yi wa mahaifinsa, Malam Bala Muhammad Bono rasuwa.
Muna rokon Allah, Gizagawan da za su yi aure a gobe, Allah Ya sanya albarka a cikinsu da iyalinsu da namu baki daya. Su kuma wadanda suka rasu, Allah Ya yafe musu, Ya ba iyalansu hakuri. Mu kuma da muka rage, muna rokon Allah Ya ba mu dacewa da cikawa da ingantaccen imani, idan namu lokacin ya zo. Amin! – Gizago.
A wannan makon, ga sababbin Gizagawan da suka dace da rijista:
1-Alhaji danjuma Maikano, 07031357980 (GZG657BAU). 2-Ibrahim Ishak Swito, 08060843396 (GZG658BAU). 3-Auwal Haruna Hazaka, 08108034158 (GZG659BAU). 4-Maryam Sani Muhammad, 08145157082 (GZG660BAU). 5-Azima Sani Muhammad, 08065800624 (GZG661BAU). 6-Sharifa Nasir, 08063439954 (GZG662BAU). 7-Usman B. Adam, 08060840069 (GZG663BAU). 8-Suwaiba A. Lawal, 08102297095 (GZG664BAU). 9-Ummi Hamza, 07064436055 (GZG665BAU). 10-Auwal Yayan Fati, 08063201200 (GZG666BAU). 11-Habiba G. Hassan, 08052674798 (GZG667BAU). 12-Khuzaifa Ibrahim Mai Zantuka, 08168500428 (GZG668BAU). 12-Jamilu Garba Zamfara, 07011550367 (GZG669ZMF). 13-Auwalu Kabiru Durumin Zungura Kano, 08096224490 (GZG670KNO). 14-Musa Isah Abubakar, 07064833646 (GZG671JGW). 15-Alhaji Muhammad Zalanga, 08025078833 (GZG672JGW). 16-Muhammad Zakari Nuhu, 08066541374 (GZG673JGW). 17-Umar Haruna Gamji, 08061618082 (GZG674JGW). 18-Malam Isah Billami Hadeja, 08030502386 (GZG675JGW). 19-Mu’azu Abu Juwuziyya, 08033676355 (GZG676JGW). 20-Malam Idris Muhammad, 08064256961 (GZG677JGW). 21-Isah Ramin Hudu, 08060353382 (GZG678JGW). 22-Abdullah Matashi, 07067826238 (GZG679JGW). 23-Baita Ibrahim, 08166053999 (GZG680JGW). 24-Isma’ila A. Sabo, 08038489088 (GZG681JGW). 25-Salahuddin Salisu, 08034637748 (GZG682JGW). 26-Shehu Garba, 08039320434 (GZG683JGW). 27-Hindatu Shu’abu (GZG684JGW).