Jadon Sancho zai koma zaman aro a Dortmund
An gaza warware takun sakar da ke tsakanin Sancho da mai horarwa Erik ten Hag.
Dan wasan gaba na Manchester United Jadon Sancho na shirin koma wa tsohuwar kungiyarsa ta Borussia Dortmund da ke Jamus a matsayin aro.
Jaridar Goal.com ta ruwaito cewa, an kulla yarjejeniyar daukar aron dan wasan kan fam miliyan 2.6 bayan da aka bude kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu.
- An cafke fasto kan damfarar abokin kasuwancinsa
- Yadda ’yan fashi suka kashe mutum 4 a ‘Supermarket’ a Nasarawa
Lamarin dai na zuwa ne sakamakon gaza warware takun sakar da ke tsakanin Sancho da mai horarwa Erik ten Hag.
Bayanai sun ce har yanzu dan wasan na Ingila mai shekaru 23 ya ki amincewa da bai wa mai horarwar hakuri game da wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Tun farko dai mai horarwa Erik ten Hag ya yi ikirarin cewa Sancho ne dalilin rashin nasarar Manchester United a wasansu da Arsenal cikin watan Satumban bara.
Wannan batun ne ya sanya Sancho ya fito ya musanta kuma tun daga wancan lokaci ne dan wasan ya koma atisaye shi kadai kuma aka daina ganinsa a sahun ‘yan wasan da Ten Hag ke amfani da su.
A sakon da ya wallafa a wancan lokaci, Jadon Sancho wanda United ta sayo daga Borussia Dortmund cikin watan Yulin 2021 kan farashin fam miliyan 73, ya ce kawai Ten Hag na neman wanda zai fake da shi ne saboda tarin rashin nasarar da ya ke fuskanta.
Bayanai sun ce Borussia Dortmund a shirye ta ke ta karbi tsohon dan wasan nata cikin watan nan.