Jagoran APC ya nemi Buhari ya zabi ministoci bisa cancanta

Jagoran jam’iyar APC a mazaba ta 6 da ke unguwar Sabo cikin birnin Ibadan, Alhaji Yahya Baba Kutunga ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi aiki da ilminsa wajen nada sababbin ministoci da sauran mukamai bisa cancanta ba siyasa ba, ta yadda za su taimaka masa tsakani da Allah wajen dakile dukkan kutungwilar da […]

Jagoran APC ya nemi Buhari ya zabi ministoci bisa cancanta
Jagoran APC ya nemi Buhari ya zabi ministoci bisa cancanta

Jagoran jam’iyar APC a mazaba ta 6 da ke unguwar Sabo cikin birnin Ibadan, Alhaji Yahya Baba Kutunga ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi aiki da ilminsa wajen nada sababbin ministoci da sauran mukamai bisa cancanta ba siyasa ba, ta yadda za su taimaka masa tsakani da Allah wajen dakile dukkan kutungwilar da PDP ta kulla a baya domin hana ruwa gudu ga mulkinsa.

Ya fadi haka ne a hira da wakilinmu jim kadan bayan kammala taron ’yan Arewa magoya bayan APC da suka yi a ranar Talata da ta gabata, domin tattaunawa a kan irin gudunmawar da za su bayar ga bikin shirin rantsar da Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo zango na biyu.
Ya ce: “Muna shawartar Shugaba Muhammadu Buhari ya mika al’amuransa baki daya ga Allah (swt), musamman ta fannin lura da cancanta wajen nada manyan mukamai. Ya kamata ya lura da kyau wajen zakulo mutanen kirki da suka samu kyakyawar shaidar kwatanta gaskiya da rikon amana da adalci wajen nada su bisa ministoci da sauran manyan mukamai, domin su ne masu kishin kasar haihuwarsu da suke kishin kasar da neman ci gaba amma ba baragurbin ’yan siyasa ba. Muddin aka yi nade-naden mukamai bisa lura da siyasa ba cancanta ba, to kuwa za mu koma gidan jiya ne.”
Da yake magana dangane da irin dangantakar ’yan Arewa magoya bayan APC da Gwamnatin Jihar Oyo, dan siyasar ya yi godiya ga Allah da Ya samar musu Gwamna Abiola Ajimobi, “domin tarihi ya nuna cewa ba a taba samun gwamnatin da ta janyo mutanenmu ’yan Arewa a tare da ita kamar wannan gwamnati ba. Babbar matsalar kawai da muke fuskanta ita ce irin yadda ba a daukar yaranmu ayyuka a ma’aikatun jihar bayan sun kammala karatu.”f