Jagoran barayin da suke kai hari a majami’u ya shiga hannu
Wadansu mazauna garin Kubwa da ke Abuja sun yi ta maza, inda suka tunkari wani gungun barayin da ke kai musu farmaki a wuraren sana’a ko majami’un da suke ibadar dare a daidai lokacin da suke yi wa jama’a kwace ta hanyar karbar kudadensu da wayar hannu da tsakar dare. Lamarin wanda ya auku a […]

Wadansu mazauna garin Kubwa da ke Abuja sun yi ta maza, inda suka tunkari wani gungun barayin da ke kai musu farmaki a wuraren sana’a ko majami’un da suke ibadar dare a daidai lokacin da suke yi wa jama’a kwace ta hanyar karbar kudadensu da wayar hannu da tsakar dare.
Lamarin wanda ya auku a Unguwar Kukwaba da ke garin Kubwa a karshen makon jiya, ya kai ga jikkata mutum 3 sakamakon sarar da barayin suka yi musu bayan yi musu kwace.
Wani da lamarin ya rutsa da shi da ke sana’ar shayi da aka sakaya sunansa, ya ce barayin wadanda matasa ne 3 da ke dauke da kananan makamai da suka hada da adda da gora, sun same shi a rumfarsa ta shayi, inda yake kwana tare da wadansu mutum 2 da misalin karfe 3 na dare, suka karbe wayoyinsu na hannu da kudi. Ya ce barayin sun nuna rashin gamsuwa da abin da suka ba su, sannan suka yi barazanar hallaka su idan suka same su da wasu kudi da ba su bayar ba.
“Sun zazzage wata jakata kuma da ba su samu kudi a ciki ba sai suka yanke ni da wuka a duwawu. Wani daga cikinsu ya ba da shawarar su kashe mu don gudun kada mu bata musu sha’ani a wuraren da za su kai hari na gaba, amma sai saura biyun suka yi ki shawarar, suka ce su bar mu tunda dai sun karbi abin da ke hannunmu,” inji shi.
Haka wani mai sayar da kayan masarufi da barayin suka yi wa kwace, ya ce mutanen sun kuma far wa wadansu mutane da ke sauke gawayi daga mota, tare da shiga wani gida da ke kan layin kafin a karshe su fada cikin wata majami’a ta ECWA, inda suka kwace wayoyi da kudin wadansu mata 7 da suke bautar dare da kuma na fastonsu. “Bayan bazuwar labarin ne a tsakaninmu sai muka hadu muka far musu a daidai lokacin da suka fito daga cikin majami’ar. Suna ganinmu sai suka tsere ta hanyar wani rafi, sai dai tare da taimakon ’yan sanda da suka kawo mana dauki daga baya-baya, sai muka gano su a wani waje suna kwance a kasa. Kuma da suka hango mu sai babban ya mike tare da yin barazana. Ganin cewa ba mu juya ba sai biyun suka tsere, shi kuma muka kama shi,” inji shi. Ya ce ’yan sandan sun wuce da jagoran barayin zuwa babban asibitin garin Kubwa, inda ake kula da shi yanzu haka.
A zantawarsa da Aminiya a asibitin, jagoran wadanda ake zargin, wanda ya bayyana sunansa da Mustafa Abubakar mai shekara 19, ya ce shi dan asalin yankin Yelwa ne da ke karamar Hukumar Dala a Jihar Kano kuma ya shafe kamar shekara daya da rabi a harkar sata, sai dai ya ce yana fata wannan da ya yi ta kasance ta karshe.
Babban Jami’in ’Yan sandan yankin Kubwa, C.S.P Ayobami Surajudeen wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kuma ofishinsu ya samu nasarar kama wadansu da ake zargi barayi ne su 3 a kwanan nan wadanda ke tare mutane a daidai lokacin da suke zuwa Sallar Asuba ko sammakon zuwa wurin aiki, su yi musu kwace ko su sare su a jiki idan ba su ba su hadin kai ba. Ya ce sun mika mutum 3 din ga Sashin Binciken Manyan Laifuffuka na ’Yan sandan Birnin Tarayya don ci gaba da bincike a kansu.