Jagoran Jagaliyar Jijjiga-ciyawa

Jagaliyar Jijjiga-ciyawa Juyin takun dan yawa Jaye-jayen ’yan adawa Ja-gaban masu dagawa Jelen juwa-juwa   Juyin aya takanda ’Yan mata sun iya gada A biki sai su rangada guda Ana ta kurda-kurda Wasu na shiga fage da sanda   Janjamin jimurda Jan zaren kadin kada Jami’in juya kauda Juyayin jin jikin kwafda Jagoran jagaliyar cuda […]

Jagoran Jagaliyar Jijjiga-ciyawa

Jagaliyar Jijjiga-ciyawa

Juyin takun dan yawa

Jaye-jayen ’yan adawa

Ja-gaban masu dagawa

Jelen juwa-juwa

 

Juyin aya takanda

’Yan mata sun iya gada

A biki sai su rangada guda

Ana ta kurda-kurda

Wasu na shiga fage da sanda

 

Janjamin jimurda

Jan zaren kadin kada

Jami’in juya kauda

Juyayin jin jikin kwafda

Jagoran jagaliyar cuda

 

Jimirin jan-kari

Jimamin batagari

Jan-ragamar bugun garari

Jarumi mai kurari

Jiniyar dan jinjiri

 

Masu wasan kulle kurciya

Ana ta kauciya

Wasu har da baudiya

Gudun shiga gida da zilliya

Zullon Zankadaziyya

 

Dandamalin dalilin taron-su

Rawar dandalin-kusu

A Jijjiga-ciyawa yai kurmusu

Shi da ’ya’yansa sun yi busu-busu

Sai ga shi yana tafka musu

 

Cancarewar carin cincirindo

Carafken dara da kwado

Rummace babban kwado

Wasu sun iya kada ’ya’yan ludo

A dai ci gaba da Dodorido

 

Gwamna gwarangwam

Jigon jangwam

Ya tauna cingam

Yai gum

Ya ki ja bakinsa kurum

 

Ya koka da taragon mai

Mara manufa takamaimai

Wai shi ga jarmai

Ya fito da makamai

karshe dai ya lashe amai

 

Jam’iyyar ’yan bumburutu

Gungun masu burunttu

Sai yawan surutu

Ga iya kulla kutu-kutu

Mabarnata a shigar burtu

 

Jam’iyya danboto da sanda jirge

Matsalolinta sun wuce kirge

Ballantana a ce an yi musu kage

Sun karke da yi wa juna goge

Suna ta gudun bera da mage

 

Miyagun sun balbalta kasa

Sun zo yi wa Baba sa-in-sa

Sun dauka mun yi na kasa

Ahir dinku ba ma wasa

Ayyukan alheri ne masu rassa

 

Kai mai suna sulalla

Da ka ga galala

Sai ka sulale da sulalla

Har ka dinka galila

Ka bar talakawa na lalala

 

Taron shekara-shekara

Matattara-matattara

Ta masu neman kasura

Da an kada kuge su zabura

Na-mujiyar kashinsu ya kangara

 

An ce mini kasan NEHU

Ni kuwa na ce kasan NA-AHU

Yadda ake yi wa matsabbai huhu

Ko ai musu daurin buhu-buhu

Jiharka ta zam huhun-ma-hu

 

Shashasha da sususu

Ga burgu da  samarin kusu

An yi turmutsutsu

Wasu sun warwatsu

Su gafiya gwanayen kurmusu

 

Sandar dansadauki

Ta kwabde masa mummuke

Mugu ya duke

Ya ji batun ba sauki

An hana shi buda baki

 

Yai kiren karya da Baba-Ojo

Yai ’yan kame-kame

Yai kememe

dansadauki ya ce kai rawar banjo

Ra’ayinka na ’yan gwanjo

 

Gallele

Mai bille

sai a kada masa talle

yai ta tsalle-tsalle

Iro ka kama shi a kulle

 

Tururuwar tolatsewa

Tabarar tabarbarewa

Takurar takurawa

Talasurun tuburewa

Tambadadden tambadewa

 

Dandalin daddalewa

Damuwar damalmalewa

Dugunzumar dagulewa

Dungun dungurewa

Damben dambacewa

 

A ranar sili da madambaci ga watan Janyen-wurin shekara ta dubu karamin lauje da sili da madambaci, an gudanar da DANDAZON DANDALIN DADDALEWAR DALILIN-TARON-SU, inda aka rakito tshon Gwamnan Jihar Jijjiga-ciyawa ya yi surutu rututu, har ya nemizarta kamfanin dillancin labarai na Reuters. Domin saboda kwarewarsa a buruntu da babatu sai ya rika mnuna cewa tabargazar da suka tafka a mulkinmulaka’u na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge a tsawon shekara sili damanuniyar sama wai Baban-burin-huriyya ya yi abin da ya dara nasu. Ni kuwa na ce ai wannan SHAIDAR ZUR ce da ZUkI-TAMALLE KAMA-KARE KA HAdA-SHI -DA -ZOMO.

barambarama da babatun Gwamna mai sunan sulalla kan dandamalin Dalilin-taron-su na shekara-shekara, inda ya hantari Baban-burin-huriyya, ba wani abu ba ne illa BUSHIYA KE SON YI WA KUNKURU kAFA. Domin a zamanin jan-ragamar Jam’iyya mai danboto da sanda jirge an shafe shekaru da sili da manuniyar sama ana ta tsuwurwurta kwakyariya wajen jkuya akalar kasar nan. Kuma sanin kowane ba taba yin kashi kwaraf da dukiyar al’umma ’a, kamar zamanin mai dan boto. Sannan shi tsohon Gwamnan Jihar Jijjiga-ciyawa Mai sunan Sulalla ya sanm cewa, Iro Mugun Madambaci ya taba dumfararsa, inda ya hada da ’yan lelensa ya garkame.

Abin farin ciki game da kwamacalar tsohon Gwamna Mai sunan Sulalla shi ne, wani Gwarzon gwaraza ya tunkare shi. Wannan gwarzo kuwa shi ne dansadauki, wanda ya fafata da Jagoran Jagaliyar Jijjiga-ciyawa, inda ya nusar da shi cewa kiren-karairayin da ya kago cewa su suka kawo Baba-Ojo mai-gonakin Ottawa ya jagorranci kasar nan zuki-ta-malle ce kama kolo ka hada shi zomo. Domin a wancan zamanin an ce ma har adawa ya yi da Baba-Ojon da yake tutiyar cewa gwaninsa ne. Kuma an tabbtar mini da cewa wata jarumar Zankadaziyyar ’yar wasan Majigin Nalelen-audu da aka gayyato wajen taron, ta tabbatar da cewa da tsohon Gwamna Mai suna sulalla wanda ya sulale da sulalla har talakawansa suka ji a salansa, ta ce da zai shiga wasan majigi tabbas da ya fita yin shuhura.

Ni dai a farfajiyar wannan makaranta ba na son a hantari dan jagaliyar jihar Jijjiga-ciyawa, don haka ba zan bai wa Gwamna Bandirawo da ke kan karaga hasken abin da ya kamata ya aiwatar ba. Don haka ina fatan za a nusar da Jagoran jagaliyar Jihar Jijjjiga-ciyawa cewa yana da abin kai wa baki don dundume kururu idan ya kokarta ya yunkura ya kutsa kai cikin hada-hadar shirin majigi. Kodayake dai ba ma son a rika dura ashariya, don kada ya koya wa ’yan dugwi-dugwi ’ya’yan Inna da Baba.

Batu na ingarman karfen karafan ytaragon kwangirri titin layin dogo mu nusar da dattaban kwabo ko na taro da sisi kanlallai su daina jagwalgwala mana siyasa tamkar sun ci naman jangwalagwada. Ahir dinku ’yan Jagaliyar Jihar Jijjiga-ciyawa. Gani ga wane dai babban darasi ne, domin idan har Jagoran Jagaliyar Jijjiga-ciyawa ya lura ai Baban-gada-gada na Jihar Ni-na-ja, wanda ya tsuwurwurta Mina-mina a wajen jan ragamar talakawa ya ja bakinsa alekum. 

Da fatan duk sa’adda masu tsuwuwrta wasannin majigi suka shiriya HAUROBIYANA, to akwai bukatar su jero tsohon Gwamna Mai sunan sulalla a matsayin fitaccen dan wasan kwaikwayo da kan garzayo ya kewayo ya yi ninkayar iyo, har masu baje na-mujiya su rika yi masa oyoyo, a duk sa’adda ya mazayo.

Muna taya Ja-gaban jagaliyarjijjiga-ciyawa murnar samun damar SUKA-DA-BURTSATSEN MAGANGANU, tamkar tsirin tsiyatakun tsinannu, wadanda suka murtuke fukar shan kunu kamar suna fama ciwon KURKUNU. Baban-burin-huriyya a yi musu sakiya,tare da shayar da suruwan UNGURNU, ko sun ytsahirta da walagigi, har su zamto ZAUNANNU!

Shi dai duk zakaran da da Mai-duka ya nufa da carar da ta zarta kyarkyarar kaza, to zai kara kazar-kazar, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.