Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Ahmed al-Sharaa, ta naɗa Murhaf Abu Qasra jigo a ƙungiyar HTS, da ta jagoranci rikicin da ya kifar da gwamnatin Bashar al-Assad, a matsayin ministan tsaro.

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sabuwar tutar kasar Syria mai tauraro uku da ‘yan adawa suka kaddamar.

Jagoran gwamnatin riƙon kwaryar Syria, Ahmed al-Sharaa ya ce, bayan samar da sabon tsarin taron ƙasar da za a yi, za su tabbatar da cewar dukkan makaman da ke hannun jama’a sun dawo ƙarƙashin ikon gwamnati, a ƙoƙarinsu na ganin an rushe ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai don shigar da su cikin run dunar tsaron ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Ahmed al-Sharaa, ta naɗa Murhaf Abu Qasra jigo a ƙungiyar HTS, da ta jagoranci rikicin da ya kifar da gwamnatin Bashar al-Assad, a matsayin ministan tsaro.

“Ba za mu barar makamai a hannun jama’a ba, ko daga ɓangaren ƴan tawaye ko kuma a ɓangaren mayaƙan Kurdawa na SDF.”

Fira ministan Syria Mohammed al-Bashir ya ce a wannan makon ne za a sake fasalin ma’aikatar tsaron ƙasar, ta hanyar shigar da ƙungiyoyin ƴan tawayen da suka kifar da Assad da tsofaffin jami’an sojin gwamnatinsa cikin rundunar sojojin ƙasar.

Haka nan a ranar Asabar data gabata, gwamnatin Syria ta naɗa Asaad Hassan al-Shibani a matsayin ministan harkokin wajen ƙasar, a wani mataki da sabuwar gwamnati ta Syria ke ɗauka don kulla hulɗar alaka da ƙasashe.

Sakamakon irin makatan da gwamnatin ke ɗauka dai ya sanya mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka Barbara Leaf, ta sanyan da matakin Amurka na janye batun bada tukuicin dala miliyan 10 da a baya ta sanar ga duk wanda ya taimaka da bayanan da suka kai ga kama Ahmed al-Sharaa.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Tags