Kasashen WajeLabarai• Created September 9, 2023 08:15
Jagoran yaki da zaluncin turawa a Afirka ta Kudu ya rasu
Shugaba a kabilar Zulu kuma jagoran yaki da wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu, Mangosuthu Buthelezi, ya rasu yana da shekaru 95.
Jagoran yaki da wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu kuma shugaba a kabilar Zulu, Mangosuthu Buthelezi, ya rasu a safiyar Asabar yana da shekaru 95.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ne ya sanar da rasuwar Mangosuthu Buthelezi, dan gwagwarmayar da ya jagoranci boren bakaken fatar a Afirka ta Kudu da ya kawo karshen mulkin danniya da turawan mulkin mallaka a kasar a shekarar 1994.
“Na kadu da rasuwar YarimA Mangosuthu Buthelezi … Firaministan Masarautar Zulu da ma kasa baki daya, wanda shi ne uban jam’iyyar Inkatha Freedom Party.”Yarima Mangosuthu Buthelezi jagora ne abin koyi a fannin siyasa da raya al’adun kasarmu, musamman wajen gwagwarmayar samun ’yancin kai a 1994 da kuma kafuwar dikomuradiyya,” in ji Shugaba Ramaphosa.Buthelezi babban basarake ne a kabilar Zulu, wadda ita ce kabila mafi yawan al’umma a kasar Afirka ta Kudu.Shi ne kuma Firaministan garin kabilar, wato KwaZulu, kuma wanda ya assasa jam’iyyar Inkatha Freedom Party, ta ’yan kabilar Zulu.