Jahilci da gidadanci ke janyo mutuwar mata a kan gwiwa – Maryam Sallau

Hajiya Maryam Muhammadu Sallau Jakadiyar cikin garin Legas, kwararriyar ma’akaciyar lafiya ce, a hirarta da Aminiya ta bayyana dalilan da ke jawo yawaitar mutuwar  mata a lokacin haihuwa da hanyar magance haka: Za mu so ki gabatar mana da kankiSunana Hajiya Maryam Muhammad Sallau, Jakadiyar cikin garin Legas da yankin  Iwaya.   Ni  ’yar asalin garin […]

Jahilci da gidadanci ke janyo mutuwar mata a kan gwiwa – Maryam Sallau
Jahilci da gidadanci ke janyo mutuwar mata a kan gwiwa – Maryam Sallau

Hajiya Maryam Muhammadu Sallau Jakadiyar cikin garin Legas, kwararriyar ma’akaciyar lafiya ce, a hirarta da Aminiya ta bayyana dalilan da ke jawo yawaitar mutuwar  mata a lokacin haihuwa da hanyar magance haka:

Za mu so ki gabatar mana da kanki
Sunana Hajiya Maryam Muhammad Sallau, Jakadiyar cikin garin Legas da yankin  Iwaya.   Ni  ’yar asalin garin Maiduguri ce a Jihar Barno amma an haife ni a garin Jos  a  1960.   A  can na yi makarantar firamare daga 1963 zuwa 1971 daga nan na je Kwalejin Koyarwa ta Mata a garin Akwanga da ke Jihar Nasarawa a yanzu, a  1977.   Daga nan na koma Maiduguri  na yi jarabawar share fagen shiga makarantar koyon aikin  ungozoma, da na samu nasara sai na bar  karatun da na soma a Kwalejin Koyarwar na ci gaba da karantar aikin kula  da karbar haihuwa  domin a wancan lokaci a Arewa iyayen yara ba sa son tura ’ya’yansu su karanci wannan fannin, don haka aka yi ta wayar wa dalibai kai a kan muhimmancinsa.
Bayan na gama a 1980 sai aka tura ni Babban Asibitin garin Gashuwa wanda a yanzu yake a Jihar Yobe na yi aiki na tsawon shekara biyu sannan na yi aure, sai aka mayar da ni Maiduguri a 1983.  Bayan na yi aiki na wata 6  sai na koma makaranta domin karo ilimi.   Na karanci fannin kula da marasa lafiya baki daya maimakon karbar haihuwar da na karanta a baya. Bayan na kammala cikin shekara daya a 1985  sai na ci gaba da aiki a babban asibitin garin Maiduguri daga nan kuma na samu aiki da wani asibiti na jami’an tsaron Najeriya a Legas a  1990 zuwa 2005,  bayan nan na samu aiki da da wani asibiti mai zaman kansa a Unguwar Ikoyi a Legas a matsayin babbar jami’ar lafiya wato ‘matron’ daga nan kuma na samu aiki da kungiyar nan ta likitoci masu aikin sa-kai na duniya, wato Doctors Without Borders, sun zo ne daga kasar Sifen.  Na yi aiki da su a Legas a shekarar 2010 zuwa 2013 bayan da aikin su ya kare, sai suka damka asibitin nasu a hannun karamar Hukumar Yaba a Legas sai aka rike kalilan daga cikinmu aka ba ni shugabancin asibitin wanda ake kira Ayetoro Primary Health Care  wato asibitin Karkara na Ayetoro kuma a nan nake aiki har yanzu.

 Me ya ba ki sha’awa  kika koyi aikin karbar haihuwa?
Da farko ina karama aikin ’yan sanda ne yake burge ni kuma shi na yi sha’awar yi saboda in na ga matansu sun sanya hular nan tana ba ni sha’awa, to lokacin da aka kai ni a dauke ni a aikin sai aka ce na yi karama ba a dauke ni ba. Daga nan ne na koma Maiduguri sai na ga makarantar koyon aikin karbar haihuwa na yi sha’awa aka karbar min fom na cike na yi jarabawa na samu, na kuma yi farin ciki da wannan aikin domin kullum cikin taimakon jama’a nake, ko ina gida ko ina  asibiti ko ina tafe a bisa hanya, don akwai lokacin da na gamu da wadansu mutane a Legas dan uwansu yana cikin matsanancin rashin lafiya za su sa shi a mota su kai shi Katsina, a lokacin na tsaya na duba shi muka tafi da su na rubuta musu magunguna aka ba shi abinci na yi masa allurai yadda zai samu saukin ciwon kafin su kai gida. Bayan na bar su da na kira su in ji yanayin jikinsa  sai ga shi ya daga waya yana min godiya har ya wartsake, nan na ce ya je asibiti in ya je gida a kara kula da lafiyarsa.

Kin  shafe  sama da shekara 30 kina aiki a bangaren karbar haihuwa, me ke jawo yawaitar mutuwar mata a lokacin haihuwa?
Akasari rashin wayewa ce  da karancin ilimi  ke janyo yawan mace-macen mata a kan gwiwa.  Sau da yawa za ka ga an kyale mace ta dade tana nakuda ba tare da an kai ta asibiti ba, daga nan sai ka ga an samu matsala kan yaro bai sauka ba an yi ta nakuda kwana da kwanaki in an samu ta haihu sai ka ga kafa ta shanye, fitsari na yoyo.  Wannan duk rashin zuwa asibiti ne ke jawo wa. Zai yi wuya macen da ta haihu a asibiti ta kamu da cutar yoyon fitsari. A yanzu ana yawan wayar wa mutane kai, ana yin shela cewa a rika zuwa asibiti ana  sanar da su cewa dogowar nakuda a gida  ba ta da amfani, a haka irin wannan wayar da kai da muke  yawan yi yana kawo saukin lamarin domin a lokacin da nake Arewa mukan je kauyuka da rugagen Fulani mu wayar musu da kai a kan muhinmancin zuwa asibiti. A wancan lokacin a garin Gashuwa wata Bafillatana haihuwar ta tara da ta zo ta goma sai ga shi ta haifi ’ya’ya uku  ka ga wayar musu da kai da ake yi shi ya sa yanzu suke zuwa asibiti in sun tashi haihuwa.

Wace  shawara za ki bai wa mata a lokacin da suke dauke da juna biyu?
Shawarar da zan ba su ita ce duk lokacin da ciki ya shiga su yi kokari su je asibiti  domin a yi awo a gane kwanciyar yaro koda bai kwanta daidai ba, za a ba su magani bayan wata daya  za ka ga ya juya, in kuma ya kai wata bakwai bai juya ba, to za a tura su babban asibitin da ya kamata a karbi haihuwar, ka  ga amfanin zuwa asibiti da wuri ke nan. Ba sai lokaci ya kure ba, tunda wuri za a rika binciken lafiyar uwar idan jininta ya yi kasa a ba ta magungunan da za su taimaka mata, amma jahilci da gidadanci ke sanya wadansu kin zuwa asibiti, haka in haihuwa ta zo da tangarda sai ka ga an mutu wadansu kuma sai an wahala an jigata daga karshe sannan su je asibitin a kurarran lokaci duk wannan ne ke janyo yawan mace-mace.

Ana samun kananan asibitoci masu zaman kansu da dama musamman a Kudu wadanda galibinsu ba su iya daukar kwararrun ma’aikata, wace irin barazana hakan ke janyo wa ga lafiyar iyali?
Irin wadannan asibitocin ba su dace ba, don haka ake da hukuma mai kula da wannan. Ita wannan hukuma alhakinta ne ta tabattar asibitoci masu lasisi ne suke kula da lafiyar jama’a,  kuma ta tabbatar da ana daukar kwararrun ma’aikata. Sannan ya kamata su kansu mutane su san inda za su rika zuwa don a duba lafiyarsu, ba kowane asibiti ba ne za ka kai kanka a duba, sai wanda ya dace, domin wadansu ma’aikatan ba karantar aikin suka yi ba, su ne za ka ga sun yi allura kafa ta shanye da makamantan haka.

 Aikin karbar haihuwa abu ne da ya shafi mata kai-tsaye, ko kin gamsu da yawan matan da ke cikin aikin?
A gaskiya ban gamsu da adadin matan da ke aikin karbar haihuwa ba. Kamata ya yi mata su tashi su yi karatu, su samu kyakyawan sakamako su koyi aikin kula da lafiya da karbar haihuwa domin su taimaka wa al’umma domin shi wannan aikin taimako ne.

Yaya za ki kwantanta ci gaban da aka samu a fannin lafiya a yanzu da a lokacin da kika fara aiki?
A gaskiya an samu ci gaba da dama domin a yanzu akwai kayayyakin aikin da a da babu su.  Musamman ma a nan Legas a lokacin da na dawo da aiki na na ga bambanci kwarai.  A lokacin da nake aiki a Arewa za ka ga yara na ta mutuwa kamar kaji, da an kawo yaro jikinsa ya yi zafi sai ka ga yaro ya mutu amma da na zo Legas da aiki sai  na ga yadda ake kulawa da su.  Ashe zazzabin cizon sauro ne ke shiga kwalkwaluwarsu,  to, a nan suna da kwarewa su yi gwaje-gwaje a ba su kulawa ta musamman sai ka ga yaro ya ji sauki ya warware.  Kazalika cinkoson da ake samu a asibitocinmu na Arewa ta yadda za ka ga da zarar mace ta haihu sai a sallame ta bayan awa biyu, wannan ma yana taimakawa wajen kamuwar zazzabi, jiki ya yi  kore nan take ka ga ya mutu, amma a nan Legas in mace ta haihu ba a sallamarta har sai bayan kwana biyu, to, a haka ne za a samu cikakkiyar kulawa da yaron da mahaifiyarsa. Bayan an yi gwaje-gwaje in an gano  da wata matsala sai a yi maganinta kafin a sallame su.

Yaya aikinki ya kasance da kungiyar likitocin nan kasa da kasar?
A lokacin kungiyar likitocin sun zo Najeriya ne daga kasar Sifen suka zabi wani wuri da wadansu al’umma suke rayuwa a bakin ruwa a Legas.  Yawancinsu marasa galihu

a nan ne muka yi aiki da su na kula da jama’ar yankin abin da ya shafi karbar haihuwa ko hadari koma dai wane irin ciwo duk a kyauta. Sannan in mace ta haihu suna tallafa mata da abin da za ta daura da kayan abinci, mutanen kasar Sifen din su suke taimakawa da kudaden aljihunsu, to a lokacin da aka fara samun matsalar tabarbarewar tattalin arzikin duniya sai suka dakatar da aikin suka koma amma yanzu haka sun dawo Najeriya sun zabi su yi aikin a Jakusko a Jihar  Yobe sun tuntube ni kan in yi aiki tare da su amma ban amsa ba, saboda yanayin wadannan yankuna a yanzu, a hakikanin gaskiya wannan kungiya ta taimaka wa jama’a sosai a Legas.

Wane alfanu kika samu a wannan aiki na kula da lafiyar iyali?
Babban alfanun aikin namu shi ne aiki ne na taimakon jama’a, muddin mutum ya kyautata niyya ya kuma yi kyakyawar mu’amala da jama’a, to muhimmin amfanin da zai samu shi ne ladansa a wajen Allah.  Na kuma gode wa Allah tunda nake karbar haihuwa sama da shekara 30 babu macen da ta taba mutuwa a hannuna.   Sau tari ana samun jami’an kiwon lafiya marasa imani masu cin zarafin marasa lafiya, za ka ga suna kyamar mace in ta zo haihuwa, duk wannan ba dabi’a ce mai kyau ba.  A lokacin da muke aiki da Turawa da zarar sun gane ma’aikacin lafiya na kyamar jama’a ko yana muzguna wa marar lafiya nan take za su sallame shi.

Sarkin Hausawan Legas Alhaji Sani Kabiru  ya nada ki Jakadiya ko yaya aka kai ga haka?
Baya ga taimakon da nake yi wa al’umma a fannin lafiya, nakan taba harkar siyasa, ina kuma taimaka wa jama’a da arzikin da Allah Ya yi min gwargwadon iko, da dai makamantan haka.  Irin wannan dan kokarin da ya ga ina yi ne aka ba ni wannan sarauta, kuma a yanzu burina baya ga taimakon da nake yi a fannin lafiya, ina shirye-shiryen yadda zan taimaka wa mata musamman matanmu ’yan Arewa mazauna Legas kan yadda za su dogara da kansu, za mu yi hadin gwiwa da Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Legas don a rika agaza musu.

To a bangaren iyali fa?
Allah Ya albarkaci aurenmu da maigidana Alhaji Muhammadu Sallau da ’ya’ya hudu maza biyu mata biyu.