Jahilci ke kawo rashin zaman lafiya a kasar nan – Sarkin Saminaka
Mai martaba Sarkin Saminaka a Jihar Kaduna Alhaji Muhammad Musa Sani ya ce jahilci ne kahin bayan rashin zaman lafiya da tabarbarewar tsaro da ake fama da shi a kasar nan.Sarkin ya bayyana haka ne a wajen bikin raba kyaututtuka da gabatar da jawabai na makarantar Saminaka Academy da ke garin Saminaka.Sarkin ya ce “Babban […]
Mai martaba Sarkin Saminaka a Jihar Kaduna Alhaji Muhammad Musa Sani ya ce jahilci ne kahin bayan rashin zaman lafiya da tabarbarewar tsaro da ake fama da shi a kasar nan.
Sarkin ya bayyana haka ne a wajen bikin raba kyaututtuka da gabatar da jawabai na makarantar Saminaka Academy da ke garin Saminaka.
Sarkin ya ce “Babban abin da ya kawo mana matsalar rashin tsaron da muke fama da shi a kasar nan, shi ne jahilci.” Don haka ya yi kira ga al’ummar Saminaka da kasa baki daya su rungumi neman ilimi.
Sarkin wanda Wakilin Makarantar Saminaka, Alhaji Lawal Ibrahim ya wakilta ya mika godiyarsa ga wanda ya kafa makarantar tare da kira ga masu dukiya su yi koyi da wannan kokari da ya yi, ta hanyar gina irin wadannan makarantu a yankin.
Babban Bako mai jawabi a taron babban likitan asibitin Saminaka, Dokta Iliya Bulus ya ce makarantar tana bada gudunmawa wajen ilimintar da al’ummar yankin. Ya yi kira ga makarantu masu zaman kansu su tashi tsaye wajen inganta makarantun, ta hanyar samar da ajujuwa da kujeru da kwararrun malamai domin a rika samun kyakyawan sakamako.
Dokta Iliya ya yi kira ga daliban makarantar su rungumi karatun likitanci domin aiki ne na ceton rai.
A jawabin wanda ya gina makarantar, Alhaji Bala Yunusa Dini ya ce ya bude makarantar ce a shekara ta 2005, domin ya bada gudunmawarsa wajen ilimintar da al’ummar yankin. Ya ce a yanzu akwai dalibai sama da 500 a bangaren firamare da sakandire na makarantar.
Ya yi kira ga al’ummar Saminaka da kewaye su kara ba shi goyon baya da hadin kai, domin ya dada inganta makarantar.