Jahilci ne a ce ni ba dan Jam’iyyar APC ba ne – Stanley Buba

Nada tsohon Shugaban karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa Mista Stanley Buba a matsayin shugaban riko na Jam’iyyar APC a jihar da aka yi kwanakin baya, ya tada kura inda wasu ’ya’yan jam’iyyar ciki har da Mataimakin Gwamnan Jihar suka ce Stanley ba dan asalin jam’iyyar ba ne. wakilinmu ya gana da Stanley Buba a […]

Jahilci ne a ce ni ba dan Jam’iyyar APC ba ne – Stanley Buba

Nada tsohon Shugaban karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa Mista Stanley Buba a matsayin shugaban riko na Jam’iyyar APC a jihar da aka yi kwanakin baya, ya tada kura inda wasu ’ya’yan jam’iyyar ciki har da Mataimakin Gwamnan Jihar suka ce Stanley ba dan asalin jam’iyyar ba ne. wakilinmu ya gana da Stanley Buba a garin Akwanga game da batun da kuma wasu batutuwan siyasar jihar:

Mista Stanley Buba Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar NasarawaAminiya: Yallabai ka ba mu takaitaccen tarihin siyasarka. 

Stanley: Ni akitec ne kuma dan siyasa. Na rike mukamin Shugaban karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa sau biyu daga shekarar 2004 zuwa 2015. Na kuma yi Sakataren kungiyar Shugabannin kananan Hukumomi (ALGON) ta jihar nan sau biyu. A yanzu kamar yadda ka sani, ina rike da mukamin shugaban Jam’iyyar APC ta jiha.
Aminiya: Yaya za ka bambanta aikinka na shugaban karamar hukuma da na jam’iyya a yanzu?
Stanley: Ba zance akwai bambanci ba, domin duk sun kunshi siyasa ce. Shugaban karamar hukuma aikin da nake yi a karkashin jam’iyyar siyyasa ce. Kamar a ce a gida daya ne, da kana wani daki yanzu kuma ka koma wani daki daban, ka ga duk a gidan ne. Kuma aikin da nake yi bayan siyasa shi ne akitec na zane-zanen gini da ya kunshi shirye-shirye da Bature ke kira ‘planning.’ Shi ya sa nake son yin amfani da hikimar da Allah Ya ba ni in zana kyakkyawar makoma ga wannan jam’iyyarmu APC a jihar nan don samun nasarori.
Aminiya: Ko za ka bayyana kadan daga cikin ayyukan da ka sa a gaba a matsayin shugaban Jam’iyyar APC?
Stanley: Kamar yadda ka sani Jam’iyyar APC sabuwar jam’iyya ce. Kadan daga cikin ayyuka na yanzu shi ne muna shirye-shiryen rajistar asalin ’ya’yan jam’iyyar ne, domin kowa ya samu katin shaidar dan jam’iyya. Na biyu kuma za mu zo mu nada wadanda za su wakilci wannan jam’iyya a mazabun unguwanni zuwa kananan hukumomi zuwa jiha. Haka muna shirin kafa wani kwamiti da zai rika sa ido a harkokin jam’iyya a jihar nan. Ka ji kadan daga cikin shirye-shiryen da muke yi ke nan a cikin ’yan kwanakin da muka shigo ofis.
Aminiya: Kwanakin baya, tsohon Gwamnan Jihar nan Sanata Abdullahi Adamu ya furta cewa Jam’iyyar APC bai kamata a ce ta fara tunanin lashe zabe a shekarar 2015 ba, domin a cewarsa jam’iyyar ba ta shirya ba. Me za ka ce game da haka?
Stanley: Wannan dai magana ne kawai irin na siyasa ya yi, don kowa na da nasa jam’iyya. Saboda haka ka ga dole yayi irin wannan magana. Kamar yadda Hausawa ke cewa ba wanda zai ce miyar mahaifiyar sa ba dadi. Amma maganar gaskiya ita ce duk wanda ya lura da siyasar Najeriya a yau, bari in ba ka misali, APC tana da gwamnoni 11 ita kuma PDP tana da gwamnoni sama da 20, yanzu kusan bakwai sun ce za su koma APC daga PDP. Ka ga idan aka ware bakwai ga wasu biyar kuma da suka ce za su bi su, idan ka duba tafiyar da akeyi ya nuna cewa PDP a kasar nan ta kare. Na biyu kuma idan ka lura a Majalisar Tarayya duk lokacin da akayi zabe za ka ga yawan ’yan PDP ya ragu don jama’a ba sa jin dadin mulkin jam’iyyar. Mu kanmu da ka gani yau muna APC daga PDP ne. Saboda haka magana ne kawai ya yi ta siyasa.
Aminiya: Nada ka da aka yi kwanakin baya a matsayin shugaban Jam’iyyar APC a jihar nan ya tada kura, wasu ’ya’yan jam’iyyar ciki har da Mataimakin Gwamna Damishi Barau sun koka cewa kai ba asalin dan jam’iyyar ne ba, me za ka ce?
Stanley: Ni dai na dauki lamarin a matsayin wauta da jahilci. Me ake nufi da mamban jam’iyya? Dokar siyasar Najeriya ta nuna cewa duk wanda ke bukatar shiga ko canja jam’iyya, yana da damar yin haka. Na biyu kuma lokacin da ake maganar hade jam’iyyu, ni kadai ne na kafa wata kungiya da ake kira “Secure Nasarawa State Organizaition,” inda muka za ga garuruwa da kauyukan jihar nan kai har taron manema labarai na yi a kan cewa a dawo Jam’iyyar APC. Akwai wani kwamitin matasan Jam’iyyar APC da Janar Muhammadu Buhari ya kafa kafin ma a hade, wanda ni na zama Mataimakin Shugaban kungiyar. Duk wadannan ayyuka mun yi da wasu daga cikinsu masu zargin wasu kwata-kwata ba a yi da su ba. Saboda haka ba ni kadai ba duk wanda ya daga yatsa ya nuna wa wani cewa shi ba dan APC ba ne, ina ganinsa a matsayin jahili ne bai da ruhun hadewa jam’iyyun. Kuma wadannan mutane da ke zargin idan ka yi bincike a kan siyasarsu za ka ga cewa sun yi sa’a ne kawai babu wata sadaukarwa da suka yi wa jam’iyyar da ta ba su damar cin zabe.
Aminiya: A karshe ko kana da wani kira da za ka yi wa ’yan jam’iyyarku ta APC da al’ummar jihar nan?
Stanley: Abin da kullum nake gaya wa mutane shi ne maganar yin amfani da bindiga ko ’yan sanda ba shi ne tsaro ba. Tsaro shi ne al’ummar kasa su ce suna son zaman lafiya kuma su yi haka ta hanyar hakuri da juna. Idan ana haka su ma jami’an tsaro an rage musu aiki ke nan. Saboda haka ina rokon al’ummar jihar nan su tabbatar da cewa sun rungumi zaman lafiya da junansu a koyaushe su fito su ba Jam’iyyar APC kuri’un su a zabubbuka masu zuwa don ceto su daga mummunar shugabanci da ake fuskanta a kasar nan a halin yanzu.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50