Jahilci ne tushen talauci a Arewa

A kwanakin baya ne aka ji Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II yana cewa yawan aure da mutanen Arewa suke yi babu lissafi ne ya sanya talauci ya yi kanta a yankin. Mai martaba Sarkin wanda ya bayyana haka a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, ya yi hasashen […]

Jahilci ne tushen talauci a Arewa

A kwanakin baya ne aka ji Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na II yana cewa yawan aure da mutanen Arewa suke yi babu lissafi ne ya sanya talauci ya yi kanta a yankin.

Mai martaba Sarkin wanda ya bayyana haka a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, ya yi hasashen cewa nan da shekara 20 zuwa 30 yankin Arewacin kasar nan zai shiga mawuyacin hali matukar ba a gyara yadda ake tafiya ba.

Kamar yadda Sarkin ya nuna a Arewa ne ake samun mutum ya auri mata da yawa alhali ya san ba ya da halin kulawa da su, sai ya haifi ’ya’ya ya bar su suna watangaririya a titi, bai san cinsu ba, bai san shansu ba. Saboda haka sai ya bukaci al’ummar Arewa su rika tsayawa a auren mace guda idan ba su da karfin rike mata da yawa.

Alal hakika idan aka dubi maganar da Mai martaba ya yi sai a ce lallai akwai kanshin gaskiya, sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba, domin Mai martaba kamar bai yi la’akari da wasu matsaloli da suke addabar yankin Arewa ba kafin ya yi wannan maganar.

A yankin Arewa ana fama da karancin ilimi har yanzu, saboda akwai magidanta da dama da suke yin aure amma saboda jahilci suke tozartar da amanar da aka dora musu, ba kuma talakawa ba ne. Sanin kowa ne za ka ga magidanci ya bar iyalinsa a gida babu abincin kirki, wani babu komai da ya bar musu, amma ya je waje yana shan shayi da burodi da indomi da kwai har da nama. Da rana ma haka zai je ya sayi abinci mai rai da lafiya  ya ci shi kadai ya bar iyalinsa da tuwon masara da miya lami.

Ka ga irin wadannan mutane ba talauci ne matsalarsu ba, jahilci ne, domin suna da halin da za su iya kulawa da iyalin nasu amma sai su yi watsi da su. Wadansu kuma sukan shiga bariki ne su bar iyalin nasu cikin wahala, su kuwa suna can maraya sun mike kafa suna sharholiya, sai su dade ba su aika wa iyalin nasu da sako ba, balle kuma su ziyarce su.

Akwai wadansu kuma masu hali ne sosai, wato attajirai ne, amma saboda jahilci sai su tura ’ya’yansu makarantar allo su bar su a can tare da malaminsu suna bara domin samun abin da za su ci, kuma su hana su zuwa gida sai sun dade sosai, saboda a tunanin irin wadannan iyaye, sai ya yaro ya yi bara, ya sha wahala ne sannan karatu zai zauna masa.

Ga alama Mai martaba ya manta da irin mazan nan da suke da mace daya amma su tsallake su gudu su bar ta da ’ya’ya, ka ga ba auren mata da yawa suka yi ba, amma ga shi dayan ma ta gagare su rekewa, me ya jawo haka, rashin sanin hakkin aure ne.

Saboda haka kamata ya yi a himmantu wajen samar da ilimi na addini da zamani ga al’ummar Arewa, domin duk inda ake da masu ilimi da yawa talauci ba ya yin karfi sosai a wurin. Da wahala a samu mai ilimi yana fama da tsananin talauci, sai dai idan ya ki tafiya da zamani, wato ya tsaya shi dole sai ya bi tsarin iyaye da kakanni, wannan kam zai sha wahala, domin bai yi aiki da ilimin nasa ba.

Haka kuma Mai martaba Sarkin Kano a kokarin da yake na nemo wa mata da yara ’yanci, ya manta cewa akwai dimbin mata zawara da suke bukatar aure saboda rikice-rikicen da aka fama da su sun ci mazansu, suna bukatar samun namijin da za su jingina da shi domin samun saukin rayuwa, koda kuwa ba ya da karfin aljihu zai kare musu mutuncinsu. Idan kuma an samu mai kokari sai ya kare mutuncin matar da marayun da take tare da su. Ga kuma ’yan mata da yawa da suke bukatar aure, idan aka kyale su suna iya shiga mawuyacin hali.

Saboda haka akwai bukatar a himmatu wajen taimaka wa ’yan uwa domin su tsaya da kafafunsu, maimakon su rika zama a karkashin wani attajiri shekara da shekaru suna yi masa aiki a matsayin yaransa. Ba haka mutanen Kudancin Najeriya suke yi ba, suna taimaka wa mutanensu ne su mike, ba su bautar da su ba, shi ya sanya talauci yake da sauki a can, sabanin Arewa inda idan wani ya fara tasowa sai a taru a karya shi, a ce ‘shi dan gidan wane ne?’

Dole sai ’yan Arewa sun canja halayensu, shugabanni su rika yin adalci, attajirai su rika tausaya wa marasa karfi, talakawa su rika rike amana, sannan uwa uba, a rungumi ilimi na addini da na zamani, ta haka ne kawai za a rage kaifin talauci a Arewa. Amma matukar akwai hassada da kushe da kyashi, to talauci zai ci gaba da samun gindin zama a yankin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos