Jaje ga ’yan kasuwan Arewa
Assalamu Alaikum Editan Jaridan Aminiya Ina fata da ku isar min da sakon jaje ga ’yan kasuwanmu na Arewa, musamman ma ’yan kasuwan Jihar Kebbi da ma ’yan kasuwan Jihar Kano, wadanda Allah ya jarrabe su da jarrabawar gobara a kasuwanninmu a wannan mako, har ta kai ga kusan gobarar ta lashe sama da kashi […]
Assalamu Alaikum Editan Jaridan Aminiya Ina fata da ku isar min da sakon jaje ga ’yan kasuwanmu na Arewa, musamman ma ’yan kasuwan Jihar Kebbi da ma ’yan kasuwan Jihar Kano, wadanda Allah ya jarrabe su da jarrabawar gobara a kasuwanninmu a wannan mako, har ta kai ga kusan gobarar ta lashe sama da kashi 80 cikin 100 na wadannan kasuwanni Allah ya kiyaye na gaba.
Allah ya mai da arzikin da ya fi wanda aka rasa a wannan gobara a karshe ina kira ga gwamnatin tarayya dama gwamnatocin jihohin Najeriya da su hanzarta samar da kayayyakin aiki irin na gaggawa na zamani hukumar kashe gobara. Domin a gaskiya rashin kayan aiki na kashe gobara a jihohin mu ya taimaka sosai wurin wannan gobara, tunda kuwa yau idan ka duba kusan daukacin jihohin Najeriya babu wata jiha da take da irin wadannan kayan aiki da za su iya biyan bukatun jama’a irin inhar an shiga irin wannan mummunan yanayi na gobara. A Jihar Bauchi motar kashe gobara sai an turata take tashi. Yau Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Bauchi mota guda daya ce kawai take aiki; ita kanta guda dayan ma ba ta da kyau. Allah ya saukake . Ta yaya guda dayan nan za ta kawo daukin gaggawa? Lokaci ya yi da ya kamata Gwamnatin Tarayya da ma na jihohi su farka, su samar da kayan aikin hukumomin kashe gobara.
Daga Ahmadu Manager Bauchi. [email protected] 08065189242.
Kira ga hukumar ’yan sanda
Muna kira ga hukumar ’yan sandan Najeriya da ya kamata ta kafa wata runduna ta musamman da za ta maida hankali domin dakile sata ko garkuwa da al’umma da ake yi a Najeriya.
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999 [email protected]
Marhabin da shirin wadata kasa da fetur
Assalamu alaikum. Hakika muna marhabin da yunkurin wadatar da man fetur a kasarmu baki daya da karamin Ministan Mai ya yi alkawari, Domin kuwa ba zai yiwu ba a ce ga arzikin mai a kasa, amma kullum cikin wahala muke da kunci na tsadar rayuwa, Mai tsadra kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi, talaka ya kasa samun saukin rayuwa. Allah ya ba mu mafita ta alkairi amin.
Daga Hafizu Balarabe Gusau da Mahmud Salihu kaura 07035304499 [email protected].
Kasafin kudin 2016
Edita don Allah ka ba ni dama domin mika fatan ‘yan Najeriya ga Shugaba Muhammadu Buhari akan matakin farko da ya samu wanda zai ba shi damar hawa turbar da zai sauke nauyi alkawuran da ya dauka, musamman ga talakawa, na amincewar da majalisar dokoki tayi da kasafin kudin wannan shekarar ta 2016. Hakika mafi yawa daga cikin ‘yan Najeriya na hangen matsalolin da suka dabaibaye kasar sun zo karshe sakamakon wannan gaggarumin kasafin da ba a taba ganin kamarsa ba a tarihin kasar, Da wannan muke fata da addu’a ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran masu ruwa da tsaki a fannin harkokin gwamnati da su dubi halin da al’ummar Najeriya ke ciki na wahalhalu da talauci ga tsadar rayuwa, sannan su kawo hanyoyin da talaka zai samu sa’ida, Allah ya yi musu jagora amin.
Daga Adamu Aliyu Amo, Katsina Sakandare Kungiya Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina. 09097300909 [email protected]
A shawo kan matsalar man fetur
Fatan alheri Aminiya Hausa. Hakika mu al’ummar Najeriya mun yi marahabin lale da sanawar hukummar NNPC a Najeriya da ta ce za ta kawo karshen matsalar mai nan da ’yan kwanaki kusa. Tabbas abin da muka dade muna jira ke nan ganin yadda muka shiga cikin mawuyacin halin na tsadar Man Fetur a Najeriya. Muna yi wa hukumar NNPC Najeriya kyakkyawan zato. Allah ya ba su ikon cika alkawarin da suka daukar wa al’ummar Najeriya.
Daga Amin. Daga Alhaji Umar 4eber Gashua 08060009190. [email protected]
A tallafa wa ‘yan kasuwa da gobara ta shafa
Ina jajanta wa ‘yan kasuwar Abubakar Rimi Kano, tare da addu’ar Allah ya mayar musu asarar da suka yi. sannan ina kira ga Shugaba Muhammad Buhari da Gwamna Ganduje da su nemi taimakon kudi daga Gwamnonin APC da manyan kamfanoni da manyan ‘yan kasuwa na ciki da wajen kasar nan domin su tallafa wa wadanda bala’in gobara ta shafa. Domin suna cikin hali na tausayawa.
Daga Maryam Zubairu Garabasa Kazaure.
Addu’a ga ’yan kasuwa
Salam. Edita don Allah ka mika min sakon jaje na ga kanawa sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar sabon gari Allah ya tsare, ya kuma kiyaye gaba; kuma ya mayar da alkairi.Su kuwa wadanda abin ya shafa Allah ya ba su juriyar hankuri.
Daga Abdullahi Umar Giro kebbi 08032624432.
Jaje ga ’yan kasuwan Kano da Kebbi
A mika min jajena ga ’yan kasuwar Sabon Garin Kano da ’yan kasuwar birnin Kebbi, wadanda gobara ta yi musu ta’adi. Allah ya mayar musu da fiye da abin da suka rasa. Allah ya kare faruwar na gaba amin.
Daga Malam Malam mai zanen hula Gololo 08032822433.
Jaje ga ’yan kasuwa
Salam. Edita ka mika min jaje ga ’yan kasuwar Sabon Gari Kano. Allah ya mayar musu, Allah ya kare gaba.
Daga Gali Gilas Gaya 08125599520
Allah ya mayar da alheri ’yan kasuwa
Salam. Don Allah Editan Aminiya ka mika min sakon jajena ga jama’ar kasuwar Sabon Garin Kano da fatan Allah ya mayar da alkairi amin. Allah Ya mai da alheri bisa asarar da aka yi a gobarar da ta tashi ranar Juma’a.
Daga Alhaji Jinjiri na Alhaji Sha’aibu Sabon Layin, Kara Gwarzo Kano, inkiya Mile 12 Legas 08111389999