Jajircewar Dokta Belel ta yi tasiri a Adamawa

Wasan kwallon kafa na kunshe da ‘yan wasanni 26. Samun nasaran ‘yan wasa ko akasin haka ya ta’allaka ne kan hazaka da shugaban ’yan wasan ya nuna shi ne ke da alhakin  sanya su kan turbar samun nasara. Dakta Abdullahi Belel ya bai wa mara da kunya, ta hanyar nuna bajinta wajen gudanar da aikinsa […]

Jajircewar Dokta Belel ta yi tasiri a Adamawa
Jajircewar Dokta Belel ta yi tasiri a Adamawa

Wasan kwallon kafa na kunshe da ‘yan wasanni 26. Samun nasaran ‘yan wasa ko akasin haka ya ta’allaka ne kan hazaka da shugaban ’yan wasan ya nuna shi ne ke da alhakin  sanya su kan turbar samun nasara. Dakta Abdullahi Belel ya bai wa mara da kunya, ta hanyar nuna bajinta wajen gudanar da aikinsa a matsayin shugaba.
Jajircewar Dokta Abdullahi Belel a fagen kiwon lafiya, ta sanya Allah Ya taimake shi ya yi tasirin kawar da cututtuka a Jihar Adamawa da kasa baki daya.
Cikin shekaru hudu da suka gabata an cimma nasarori da dama a hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko na Jihar Adamawa. Nasarori da aka samu a hukumar ta samu ne sabili da hangen nesa da shugaban hukumar ke da shi domin burinsa, ita ce ganin cibiyoyin kiwon lafiya sun habbaka a Jihar Adamawa.
Babu shakka don samun kwarewa kan aiki da cin nasara Dakta Belel ya yi karatun digirinsa na farko a fannin yakar cututtuka a Jami’ar Maiduguri, inda ya nuna hazaka da bajinta a karatunsa.
Jihar Adamawa ta yi da ce da samun haziki kamar Dakta Belel, wanda ya samu horo kan aiki yayin da yake zama matsayin mai sanin makamar aiki a asibitin koyarwa na Jami’ar Jos.
Daga nan ya tafi fitacciyar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria don kara samun ilmi, ya kuma samun kwarewa a fanin kiwon lafiya, inda ya yi karatunsa digiri na uku.
Kafin ba shi wannan mukami na shugaban hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko yana aiki ne a asibitin kwararru na jiha da ke Jimeta. Ganin kwazon da yake da shi wajen aiki, ya sanya hukumomi kamar Bankin Duniya da Majalisar dinkin da Hukumar tallafa wa kasashen duniya ta kasar Amurka daukarsa don yin aiki da su.
Bisa yadda yake gudanar da aiki a hukumar, na nuni da ya lakanci kan aiki, wanda hakkan ya ba shi damar yakar cututttuka kamar ciwon zazzabin cizon sauro da Nimoniya da Ebola da cutar gudawa da kyanda da dai sauransu.
Ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga hukumar yaki da tarin fuka da kasar Netherlands ke ba da tallafi. Ya kuma samu horo a kan yadda za a gudanar da shugabanci, wanda hakkan ya ba shi saukin aiwatar da aiki ba tare da wata tsangwama ba.
Aikace-aikacen Dakta Belel na tafiya daidai da kalamansa, domin yana sanya shugabanin addinai da sarakunan gargajiya wajen aiwatar da aikace-aikacen hukumar a yankunan karkara.
Ya samu dimbin nasararoi, wadanda suka hada da nadin da Marigayi Sarkin Bauchi Suleimanu ya yi masa. Hakan kuwa t a janyo masa karramawa daga sauran sarakuna da daga sassa daban daban zuwa masarautar. Kwanakin baya masana kiwon lafiya daga jihohi shida a yankin Arewa suka zo Yola don samun dabarun aiki na kiwon lafiya daga Dakta Belel ta yadda jama’arsu za su amfana da shi.
Dakat Abdullahi Belel na shugabantar hukumar samar da kiwon lafiya matakin farko a jihar Adamawa tun kafuwarta a shekara dubu biyu da 11 zuwa yanzu.
Bisa la’akari da gogewarsa a fannoninj kula da lafiya, ina ganin zai yi matukar fa’ida idan wannan gwarzon al’umma ya himmatu wajen koyar da al’umma, musamman dalibai irin dimbin ilimin da Allah Ya ba shi.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno