“Jajircewar Farfesa Jega na ganin an yi zaben gaskiya ya sa na wake shi”
Matashi Aminu Musa dan Auta daya ne daga cikin mawakan zamani da ke zaune a Kaduna. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana dalilansa na yi wa Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega waka bayan an kammala zaben kasa baki daya. Ga yadda hirar ta kasance: Ko za ka bayyana mana tarihinka a takaice? Sunana Aminu […]
Matashi Aminu Musa dan Auta daya ne daga cikin mawakan zamani da ke zaune a Kaduna. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana dalilansa na yi wa Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega waka bayan an kammala zaben kasa baki daya. Ga yadda hirar ta kasance:
Ko za ka bayyana mana tarihinka a takaice?
Sunana Aminu Musa dan Auta kuma an haife ni ne a Jihar Kaduna amma mahaifina mutumin Maiduguri ne, ita kuma mahaifiyata ’yar Jihar Kano.
Na yi karatun firamare a LEA Nuhu Bamalli, sannan na kammala karatun Sakandare a Kwalejin Gwamnati da ke Tudun Nufawa Kaduna.
Ko ka gaji waka daga mahaifinka ne?
Gaskiyar magana shi ba mawaki ba ne, kafinta ne shi kafin Allah Ya karbi rayuwarsa.
Me ya ba ka sha’awa da waka har ka dauke ta a sana’a?
Abin da ya ba ni sha’awa shi ne yadda jama’a ke isar da sako ta waka. Wannan ne ya ba ni sha’awa har na dauke ta sana’a. Akalla na dauki shekaru goma ke nan ina waka zuwa yau.
Wakoki nawa za ka ita tunawa ka yi a cikin wadannan shekaru?
Gaskiya da tun ina kirga yawan wakokina har na gaji da kirge saboda haka a yanzu ba zan iya fada maka yawan wakokin da na yi ba. Wakokin da na yi fice da su na siyasa ne kamar wanda na yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ahmad Muhammad Makarfi, a lokacin yana gwamna. Baya ga wannan nakan yi wakokin biki, inda cikin ikon Allah na samu karbuwa a jihoh in Sakkwato da Zamfara. Na yi wa tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato waka da kuma Zamfara yanzu, Alhaji Abdul’azeez Yari.
Game da alherin da na samu da waka kuwa, gaskiya babu abin da zan ce sai dai godiya; domin duk abin da ka dauka sana’a to in Allah Ya yarda zai taimaka maka. Na samu alheri daidai gwargwado, duk da cewa dai abin sirri ne.
A wakar da kaka yi ko kana da yan amshi ne?
E, akwai ’yan amshi mata da muke dauka suna yi mana amshi. Idan mun gama sai mu biya su dan abin da ba za a rasa ba.
Ko me ya sa ka yi wa Shugaban Hukumar Zabe Attahiru Jega waka?
Abin da ya sa na yi tunanin yi wa Attahiru Jega waka, gani na yi kasarmu na cikin wani hali na yanayin fargabar ko za a gudanar da zabe lafiya ko a’a. Kuma kusan wadanda suke ganin zaben nan ba za a yi shi lafiya ba sun fi yawa. Kuma cikin ikon Allah tare da jajercewar da ya yi sai Allah Ya sa aka yi cikin nasara. Wannan ya faru ne saboda kyautata niyyar Jega ga zaben, shi ya sa ya gudanar da abin da ya kamata. Saboda haka na ga ya cancanci in yi masa waka ba tare da ya sa ni ba, ba kuma tare da cewa sai an biya ni ba. Na yi amfani da basirata da hikimar da Allah Ya yi mini har na yi masa waka. Wannan ya sa har ta kai ga na ga ya dace da ni ma in yi tattaki daga Kaduna zuwa Abuja domin mika masa faifan wakar da na yi masa.
Wane jan hankali za ka yi wajen ganin ana ba masu sana’a irin taku daraja a kasa?
Gaskiya mawaka da masu shirya wakokin fina-finai muna bukatar matukar taimako a wajen gwamnati. Domin idan ka yi la’akari da yadda wasu mawaka suke amfana, mu sai an ce za a yi sai ka ga abin bai yiwu ba. Sai dai muna sa rai da wannan sabuwar gwamnati, da fatan za ta tuna da mu.