Jakada ya yabi hadin kai da Hukumar NAHCON

Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya ya nuna gamsuwa kan yadda ake samun hadin kai a tsakaninsa da Hukumar Hajji ta Qasa (NAHCON) a yayin shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji a kowace shekara. Qaramin Jakadan ofishin na Jiddah, Ambasada Muhammad Sani Yunusa ya bayyana haka a Makka, yayin da yake auna aikin Hajjin bana, ya ce […]

Jakada ya yabi hadin kai da Hukumar NAHCON


Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya ya nuna gamsuwa kan yadda ake samun hadin kai a tsakaninsa da Hukumar Hajji ta Qasa (NAHCON) a yayin shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji a kowace shekara.

Qaramin Jakadan ofishin na Jiddah, Ambasada Muhammad Sani Yunusa ya bayyana haka a Makka, yayin da yake auna aikin Hajjin bana, ya ce sassa uku: Ofishin Jakadacin Najeriya da ke Riyadh da Ofishin Jakadancin Najeriya na Jeddah da Hukummar Hajji ta Qasa sun kasance abokan hadin gwiwa wajen yi wa mahajjatan Najeriya hidima.

Ya ce dukan shirye-shirye wajen samar da masauki ga mahajjata da sauran harkokin da ake gudanarwa a  Saudiyya da tarruruka da musayar wasiqu da dukan hukumomin Saudiyya ana yin su ne da cikakkiyar sanya hannun ofisoshin jakadancin, inda ya yaba wa NAHCON kan tsayuwar dakan da ta yi wanda ya ce ya taimaka wajen sauqaqa duk wani givi da za a iya samu wajen sadarwa a tsakanin Najeriya da Saudiyya a kan al’amuran aikin Hajji. Ya bayar da tabbacin cewa ofishin jakadancin yana goyon bayan dukan sauye-sauyen da Hukumar NAHCON take gudanarwa domin tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya sun ci gajiyar kudinsu ta hanyar ba su kulawa mai kyau.

Jakadan ya qara nuna gamsuwarsa kan yadda Hukumar NAHCON ta tafiyar da harkokin da suka shafi huldar diplomasiyya, daya daga ciki shi ne musguna wa mahajjatan Jihar Nasarawa biyu da abin da ya biyo baya. Ya bayyana yadda aka kama wani mahajjaci mai tavin hankali daga Jihar Sakkwato kan zargin satar wani jariri, amma aka aka hanzarta sake shi bayan tsoma bakin Hukumar Kula da Alhazai  ta Jihar Sakkwato.

Alhaji Yunusa ya ce aikin Hajjin bana ya kuvuta daga matsalar safarar miyagun qwayoyi, inda ko mutum daya ba a kama da qwaya ba. Ya yaba wa hukumomin tsaro na Najeriya game da aikin da suka yi kuma ya buqace su da su kawar da abin da ya kira ‘dillalan miyagun qwayoyi’ a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Ya ce, shirin Hukumar NAHCON na tsoma dukan fannonin aikin Hajji don zama wani madaidaici na qasa, ya yayi kyau saboda yana daya daga cikin hanyoyin da Najeriya za ta iya amfani da su lokacin aikin Hajji wajen tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a qasar nan.

“Aikin Hajji, aiki ne mai tsarki da ke buqatar hadin kai da kwanciyar hankali da haquri da hada hannu. Yunqurin NAHCON ta yin komai ‘na qasa’ a lokacin aikin Hajji ya yi kyau sosai. Shirye-shiryen ciyar da mahajjata da samar da masauki a Makka da Madina da kula da lafiya da sauransu wajibi ne sun nuna alamun qasa, domin Saudiyya tana daukar Najeriya ce a matsayin wata qasa ce kamar sauran qasashe,” inji shi.

 

 

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo