Jakadan Amurka zai ba da shaida a majalisa kan badakalar ‘neman karuwai’

Majalisar Wakilai ta gayyaci Jakadan Amurka a Najeriya Mista James Entwistle kan ya bayyana a gabanta domin ya yi karin bayani a kan zargin da ya yi wa wadansu mambobinta na neman karuwai yayin wata ziyarar aiki da suka kai kasar.A watan da ya gabata ne James Entwistle ya aike wa Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara, […]

Jakadan Amurka zai ba da shaida a majalisa kan badakalar ‘neman karuwai’
Jakadan Amurka zai ba da shaida a majalisa kan badakalar ‘neman karuwai’

Majalisar Wakilai ta gayyaci Jakadan Amurka a Najeriya Mista James Entwistle kan ya bayyana a gabanta domin ya yi karin bayani a kan zargin da ya yi wa wadansu mambobinta na neman karuwai yayin wata ziyarar aiki da suka kai kasar.
A watan da ya gabata ne James Entwistle ya aike wa Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara, yana zargin ’yan majalisar uku daga cikin 10 da suka kai ziyara kasar da nuna rashin kamun kai da yunkurin yin fyade da neman karuwai.
Mista Entwistle ya ce ’yan majalisar su ne, Mohammed Garba Gololo (APC, Bauchi) da Samuel Ikon (PDP, Akwa Ibom) da kuma Mark Gbillah (APC, Benuwai), zargin da suka musanta.
Ya ce Mohammed Garba Gololo ya yi yunkurin rungumar wata ma’aikaciya da ta je gyara masa dakinsa da niyyar yin lalata da ita. “Mark Terseer Gbillah da Samuel Ikon sun bukaci ma’aikatan wurin ajiye motoci na otal din da su nemo musu karuwai,” inji Mista Entwistle.
Tun a wancan lokacin ’yan majalisar suka musanta zargin, inda suka ce a shirye suke su koma Amurka domin kare kansu. Kuma sun bukaci Jakadan ya janye zargin ko su shigar da shi kara a kotu.
Majalisar dai ta kafa kwamitin bincike, wanda ya nemi Mista Entwistle ya bayyana a gabansa domin gabatar da hujjojinsa kan zarge-zargen da ya yi.
Kakakin Shugaban Majalisar Turaki Hassan ya ce a jiya Alhamis ne ake sa ran Mista Entwistle ya bayyana a gaban kwamitin.
Sai dai har rubuta wannan rahoto Aminiya ba ta samu bayanin halin da ake ciki ba.
Shugaban Kwamitin da’a na Majalisar Nicholas Ossai, ya ce ba su gayyaci jami’an otal din da aka yi zargin ’yan majalisar sun nemi karuwai a cikinsa ba, yana ce gayyatar da suka yi wa Mista Entwistle ta wadatar.