Jaki da Kare
Assalamu alaikum Manyan gobe. Tare da fatan alheri kuma kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin Jaki da Kare. Labarin yana yin nuni ne da abin nan da Hausawa ke cewa Iya Gani, Iya kyalewa. A sha karatu lafiya. Akwai wani mai wanki da guda wanda yake da Kare da kuma Jaki. Rannan sai […]
Assalamu alaikum Manyan gobe. Tare da fatan alheri kuma kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin Jaki da Kare. Labarin yana yin nuni ne da abin nan da Hausawa ke cewa Iya Gani, Iya kyalewa. A sha karatu lafiya.
Akwai wani mai wanki da guda wanda yake da Kare da kuma Jaki. Rannan sai barayi suka shiga cikin gidansa don yi masa sata. Ganin hakan sai Karen ya rika yin haushi har ya kori barayin daga gidan. Hakan ya sa mai wankin ya jinjinawa karensa. Hatta makwabta sun jinjinawa Karen.
Wannan abin ya baiwa Jaki haushi. Sai ya ce wa kansa shi ma zai yi iya kokarin nunawa mai wankin shi ma yana da amfani.
Bayan mako biyu sai wadannan barayin suka sake shigowa gidan. A wannan lokaci Jakin ne ya gansu ba karen ba. Sai Jaki ya shiga yin tsalle da ihu har ya kori barayin. Mai wanki da jin ihun jaki sai ya samu tsumagiya ya daure Jaki sannan ya ce kada ya sake yi masa ihu da dare a cikin gida.
Daga rannan jakin ya dauki alkawarin ba zai sake sanya kansa akan abin da bai shafe shi ba, kuma ko mai ya sake gani zai yi abin nan da Hausawa kan ce ne iya gani, iya kyalewa, ma’ana ba ruwansa ko mai zai faru sai dai ya faru.
Manyan gobe kun ga a nan mai wanki ya nuna son kai, kuma ya janyo wa kansa don komai na iya faruwa.