‘Jaki da Karen daji’

Taku; Amina Abdullahi Akwai wani Jaki wadda yake a wani kauye. Kullum shi kadai yake ba shi da aboki. Ran nan Karen daji ya je wucewa ta kusa da jakin sai ya lura jakin yana cikin bakin ciki da tashin hankali.  Ko da ya tambayeshi me ke damunsa sa Jaki ya amsa masa da cewa […]

‘Jaki da Karen daji’

Taku; Amina Abdullahi

Akwai wani Jaki wadda yake a wani kauye. Kullum shi kadai yake ba shi da aboki. Ran nan Karen daji ya je wucewa ta kusa da jakin sai ya lura jakin yana cikin bakin ciki da tashin hankali.  Ko da ya tambayeshi me ke damunsa sa Jaki ya amsa masa da cewa yana neman abokin da za su rika yin abota da juna ne.

Karen daji ya ce ya amince daga ranar su zama abokan juna.  Sai suka shiga wata gonar wani manomi domin samun abinci. Bayan sun samu mangoro sun ci sun yi nak sai Jaki ya ce yanzu sun koshi saura abu daya, sai Karen daji ya ce wani abu kenan? sai Jaki ya ce waka. Karen daji na jin haka sai ya gargadi jaki Jaki da ya yi shiru domin idan manomin yaji muryarsa zai kama su.

Jaki ya ki bin shawara ya shiga waka shi ko Karen daji ya yi maza ya buya a bayan wata bishiya. Can sai ga manomi ya zo da katuwar sanda ya daki Jaki da ita Jaki ya runtuma a guje cikin daji don ya tsira.

Bayan manomi ya koma sai Karen daji ya yi wa Jaki dariya tare da cewa “wannan shi ne sakamakon rashin bin shawara”.