Jaki ko mutum?

Wata rana wani Alhaji ya biyo hanyar da ke cike da motoci, sai ya yi rashin sa’a, wani mai korar jakai shi ma ya koro jakansa. Ko da jakai suka zo kusa da motar Alhaji sai kawai suka yi masa kaka-gida. Alhaji ya rasa yadda zai yi. Da ransa ya baci sai ya ce wa […]

Jaki ko mutum?
Jaki ko mutum?

Wata rana wani Alhaji ya biyo hanyar da ke cike da motoci, sai ya yi rashin sa’a, wani mai korar jakai shi ma ya koro jakansa. Ko da jakai suka zo kusa da motar Alhaji sai kawai suka yi masa kaka-gida. Alhaji ya rasa yadda zai yi. Da ransa ya baci sai ya ce wa mai jakai: “Wai kai tsakanin kai da jakan waye jakin waye mutum?” Sai shi ma ya amsa da cewa: Alhaji ai kai ne jakin, tun da ka kasa gane tsakanin mutum da jaki har ka tsaya kake tambaya.”