Jama’a kar mu yi sakaci da katin zabe
Edita donn Allah ka ba ni dama in yi kira ga jama’a da su rike katinansu da daraja, ka da su yi sakaci wajen kula da shi, saboda mahimmancinsa. Domin kuwa katin zabe shi ne kawai zai baka damar zabar wanda kake so, kuma ita ce hanyar da za ka kawar da zalunci da mulkin […]
Edita donn Allah ka ba ni dama in yi kira ga jama’a da su rike katinansu da daraja, ka da su yi sakaci wajen kula da shi, saboda mahimmancinsa. Domin kuwa katin zabe shi ne kawai zai baka damar zabar wanda kake so, kuma ita ce hanyar da za ka kawar da zalunci da mulkin zalunci. Daga karshe nake addu’ar Allah ya kawo mana shugabanni masu adalci, ya kuma kawo mana zaman lafiya a Najeriya, da ma duniya baki daya. Daga Aminu Abdu Baka noma Sani mai nagge Kano 08099479880
Ta’aziyyar dalibai
Ya Allah ya jiakan daliban da suka rasa rayukansu sakamakon harin bam din da aka kai a garin Pataskum. Tare da bai wa iyayensu hakurin jure rashinsu. Ya Allah ka tona asirin duk mai hannu a wannan ta‘addanci da ya kici yaki cinyewa a yankinmu na Arewacin Najeriya. Daga: Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382
Jinjina ga Gwamna Kwankwaso
Gwana Kwankwaso ya yi rawar gani, wajen samar da ayyukan yi gamatasa,tare dabiyan Naira Miliyan Ddubu Hamsin50 da tsofuwar Gwamnatin Malam Ibrashin Shekarau ta ciyo. Hakika yaba kyauta tukwici. Da wannan ne nake kira ga Gwamna Rabi’u Kwankwaso da ya janye aniyar sa, ta tsayawa takarar Shugabancin Najeriya a 2015, domin Wallahi Janar Miuhammadu Buhari ya fi Cancanta da shugabancin Nigeriakasar nan. Da fatan talakawan Najeriya sun tuba daga karbar na goro a hannun gurbatattun ‘yan Siyasa. Kun ga abhin da hakan ya haifar mana. Daga Garba Nakwalo Ajaura Jihar Jigawa 08060911100
Sulhun sarkin Kano da Shugaban kasa
Mun yi mutukar farin ciki tare da murna akan sulhun da aka yi tsakanin gobnatin tarayya da Masarautar jihar Kano. Yin hakan wani babban tagomashi ne ga Mu talakawan jihar Kano, ta fanni samar mana da ayyukan yi musamman acikin gobnatin tarayya . Allah Ya ja da ran Sarki, Allah Ya karawa Sarki Lafiya, Allah Ya taimaki Masarautar jihar Kano, Ya ba mu lafiya da zama lafiya da Karuwar arziki a jihar Mu.
Daga Mansoor Said PRP Kano. 07039215954 .
Rashin tsaro a Arewa
Matsalolin rashin tsaro da yawaitar hare-hare a Arewa cin Najeriya, na nuna rashin tabbas gameda ci gaban kasar a matsayin kasa daya, al’umma daya. Idan aka yi wasa, hakan na iya haifar da yakin basasa wanda a karshe, wani yankin zai iya ballewa daga cikin kasar. Daga Mansoor Said PRP Kano. 08091401681
Za takurawa ’yan adawa a Kano
A gaskiya matakin da Gwamna Kwankwaso ya dauka na hana lika posta a gine -ginen gwamnati bai dace ba. Wani yunkuri ne na takura wa jam’iyun adawa a Jihar Kano. Daga Garba Sabiola Sa ‘idawa Gashu’a 08096284154
Ta’aziyyar daliban Potiskum
Ina amfani da wannan dama wajen jajantawa tare da isar da ta’aziyata ga al’ummar garin Potiskum, musamman wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hare-haren ta’addanci da ake kaiwa, na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai wa ddalibai yayin da ake musu asambilin, ranar Llitinin, harin da ya rutsa da rayuka masu tarin yawa. Muna rokon ka Allah ka wulakanta duk mai hannu a wannan lamari, Allah ka kawo mana zaman lafiya tabbatacce a nan Jihar Yobe da fadin Najeriya. Amin. Daga Usman bin Affan Damaturu.
Ta’aziyyar daliban Potiskum
Edita don Allah ka ba ni dama in mika ta’aziyata ga al’ummar Potiskum. Da farko deai sai dai mu ce inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un. Al’ummar garin Potiskum muna tayaku jaje sakamakon harin da aka kai a makarantar sekondiren kwana, wato Science secondary school Potiskum. Da fatan aAllah ya jikkan wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Ubangiji Allah ya kiyaye na gaba. Don haka a karshe don Allah matasan garin Potiskum ku dinga sa’ido sosai a kan masu shigowa da kuma ficewa saboda kare rayukan jama’a. Daga Sunusi London Boy Damaturu, Jihar Yobe, 08091735162.
Ga Kwankwaso
Najeriya sai dan Musa, dan majidadin Kano, hakimin Madobi. Ka yi aiki Wreka, ka yi mataimakin kakakin majalisar tarayya; ka yi zababben wakilin gyaran kundin tsarin mulki; ka yi kayi ministan tsaro; ka yi jakadan zaman lafiya a Dafur da Somaliya; ka yi memba a Hukumar kula da Yankin Neja Delta. Kuma ga shi kana gwamnan yanzu. Fatanmu ka gama lafiya, ka zo ka rike Najeriya yanzu in Allah ya yarda.
Daga Musa Inuwa 08033625757
11-11-14 ranar bakin ciki ce
Edita don Allah ka ba ni dama in isar da sakona ga ’yan uwana ’yan Najeriya. Ra’ayina shi ne 11 ga watan nuwambar 2014 da Shugaba Jonathan ya kaddamar da yakin neman zaben sa,ranar bakin ciki ce. Da wannan nake kira ga duk dan Najeriya, cewa ya kamata mu daura damarar yakin neman wargaza duk wani mai muradin kawo ka kasarmu koma baya, ta hanyar dukufa wajen rokon Allah Madaukakin sarkida fitowa ranar zabe, don kada kuri’un mu. Don haka kalubalen ki hukumar zabe, mun zura miki ido, mu gani ko za ki dawo da martabar ki, wadda aka sanki da ita da. A karshe ina mika ta’aziya ta ga ’yan uwana wadanda suka rasa rayukkansu a wata makaranta dake Potiskum, Jihar Yobe, Allah ya jikansu amin. Daga Nasiru Musa Maiyama, Jihar Kebbi 08062206733.
Addu’a ga kasa
Hakika tashin tashinar da ke aukuwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya tana da nasaba da rashin adalcin shugabanni. Domin su ne wadanda alhakin tsaron rayukan al’umma ya rataya a kansu. A karshe ina kira ga ’yan uwa ‘yan Najeriya da mu dukufa da yin addu’ar samun sa’idar rayuwa daga Allah, insha Allahu komai ya yi farko, yana da warshe. Daga Garba Nakwalo Ajaura Jihar Jigawa 08091927222.
A tausaya wa ’yan gudun hijira
Rana zafi inuwa ‘kuna ba komai ba ne yasa na fara da wannan kalamai ba, sai ganin yadda ’yan gudun hijira sama da dubu 10 ke tururuwa zawa garin Yola abin takaici ne da bakin ciki . In ka dubi halin da suke ciki. Don Allah !! masu hannu da shuni da gwamnatocin kasashe Afirka ku jikan wadannan al’ummomi don suna bukatar agaji. Daga Alhaji Umar Foreber Gashua 08108003333.
Kirarin Kwankwaso
Salam kirarin kwankwaso gaba dai, gaba dai, bangon sukari, lafiya jin dadin talakawa; lafiya mai fada da cikawa lafiya. Dodon PDP, lafiya dodon marasa kishi; lafiya uwar zuma ki tashi a biki; lafiya shaho firgita ‘yan tsaki . Allah ka taimaki Kwankwaso da mabiyansa, amin . Daga Maloli Saka-ratsa, Kano.
Ga ’yan takarar APC
Salam Aminiya ku shigar min da sakona ga masoyan Rocas da Atiku da Kwankwaso, da Buhari su hada kansu, kar su yi gaba da juna. Daga Saminu Isma’il Umar kokiya, karamar Hukumar Shanono, Jihar Kano
Addu’a ga Aminiya
Salam. Aminiya ina yi muku fatan alkhairi. Kuma ina jin dadin jaridarku sosa, domin duk makon duniya duk inda nike to Aminiya ba ta wuce ni. Allah Ubangiji ya kara muku fahimta, ya kara taimakawa. amin. Daga Isah Giwa (Dpa).
Ga asibitin Sabon-Wuse
Edita ka yi kira mahukunta su rika tausasa wa talaka a asibitocinmu. Domin na ga wata al’ada mummuna a asibitin Sabon-Wuse, inda aka bukaci lallai sai na bayar da Naira 100 sannan a yi wa matata allura, alhali a bayan mai neman karbar wannan kudin an rubuta wani sako cewa duk wanda ke da korafi, to ya kira lambar waya. Jami’an hukuma in har da gaske kuke yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, to a nusar da ma’aikatan asibiti cewar su masu tusayin al’umma ne. Daga 08033707082.
Godiya ga Muntari dandutse
Assa alamu alaikum Aminiya, don Allah ku isar min da giodiyata ga Hon Muntari dandutse da Hon Abubakar Muhammad, bisa kokarinsu na hada kanjama’a a jam’iyyar APC. Da fatan Allah Ya ida musu nufinsu. Daga Abubakar Yusuf Funtuwa Makera 08052584442.
Ga manyan Arewa
Talakawan Najeriya ba mu da mafita, illa kawai mu rungumi addu’a. Manyan Arewa kun ci amanar jama’a. zabe yana zuwa. Allah Ya kunyata azzalumai. Daga 07068223015.