Jama’a ke da damar zaben shugabannin kirki

  An bayyana cewa jama’a na da rawar takawa wajen zaben shugabannin kirki a dukkanin matakan shugabanci a fadin kasar nan. Tsohon Shugaban karamar Hukumar Dala, Mahmud Sani Madakin Gini ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayani a wani shiri a gidan Rediyon Freedom dake Kano. Mahmud Madakin Gini ya bayyana cewa matukar […]

Jama’a ke da damar zaben shugabannin kirki
Jama’a ke da damar zaben shugabannin kirki

 

An bayyana cewa jama’a na da rawar takawa wajen zaben shugabannin kirki a dukkanin matakan shugabanci a fadin kasar nan.

Tsohon Shugaban karamar Hukumar Dala, Mahmud Sani Madakin Gini ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayani a wani shiri a gidan Rediyon Freedom dake Kano.

Mahmud Madakin Gini ya bayyana cewa matukar al’umma ba za su zama alkalan kansu wajen zaben shugabanni ba, to kuwa za su ci gaba da fuskantar koma baya. “Duk mutumin da ba jama’a ne a gabansa ba, to ba za ka sa rai zai yi maka wani aiki na cigaban jama’a ba, don haka lokaci ya yi da jama’a za su bude idanunsu su zabi shugabanni masu kaunarsu wadanda za su yi musu aiki.”

“Ba yau aka fara shugabanni a kasar nan ba tun daga kan matakin karamar hukuma da jiha har zuwa kasa ba, amma idan ka dauki shugabannin nan ka auna su za ka tarar cewa fiye da kashi 70 ba al’umma ne a gabansu ba, bukatunsu ne suka dame su. Sai ka ga idan an yi zaben sun hau kujera sai su bar talakawa da shan wahala. Duk abin da zai je ya dawo sai ka ga al’ummar da ke kasa suke ji ajikinsu. Idan an zabi mutumin kirki mai mu’amala da son ci gaban al’umma, to jama’a ne za su amfana. Ma’ana idan an tashi zabe a fito da mutane masu tsoron Allah wadanda duniya ta yarda da nagartarsu, wadanda ake sa rai za su yi abin kwarai, to sai a zabe su don kwalliya ta biya kudin sabulu”

Har ial yau ya yi kira ga jama’a da su kaucewa yin zaben don dan abin da za a ba su wanda bai taka kara ya karya ba, a karshe a bar su da cizon yatsa, a maimakon haka su yi kokarin zaben nagartattun shugabanni wadanda ke da kishin al’ummarsu.

Tsohon Shugaban karamar Hukumar Dala ya ce duk da cewar al’umma su ne wuka da nama wajen zaben shugabanninsu ya kamata su ma shugabannin su ji tsoron Allah tare da rike amana wajen sauke nauyin da suka dauka wanda za su bayar da shaida na abin da suka aikata a ranar Alkiyama.

“Yawancin rashin tsoron Allah da shugabanni ba sa yi shi ne ummul aba’isin jagwalgwalewar al’amura. Ya kamata dai shugabanni su sani karshen alawa kasa. Mu tuna kafin mu karbi mulkin nan sai da muka yi rantsuwa da Alkur’ani ko Bible cewa za mu yi gaskiya tare da daukar alkawarin yin abubuwan da suka kamata, amma abin takaici sai ka ga mutum ya ajiye wannan ya shiga aikata abin da ransa ke so. Wannan ba daidai ba ne”

Alhaji Mahmud Madakin Gini ya kuma shawarci al’umma gaba daya da su hada kai tare da taimakon juna da kuma kaucewa furta kalaman batanci wadanda ka iya raba kawunan al’ummar kasar nan mai kabilu da addinai daban-daban.