Jama’a na taimaka wa Cibiyar Lafiya ta Azare – Dokta Ibrahim
Dokta Abdullahi Ibrahim shi ne Babban Daraktan Gudanarwa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Azare Jihar Bauchi wakilinmu ya zanta da shi game da halin da asibitin ke ciki da kuma abin da ya biyo bayan harin da aka kai tashar mota da ke garin: Aminiya: Wane hali ka samu wannan asibiti […]
Dokta Abdullahi Ibrahim shi ne Babban Daraktan Gudanarwa na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Azare Jihar Bauchi wakilinmu ya zanta da shi game da halin da asibitin ke ciki da kuma abin da ya biyo bayan harin da aka kai tashar mota da ke garin:
Aminiya: Wane hali ka samu wannan asibiti a lokacin da ka karbi shugabancinsa?
Dokta Ibrahim: Da ni aka bude wannan asibiti saboda haka na yi aiki da mutane daban-daban domin da yawa daga cikin wadanda muka yi aiki tare wasu malamaina ne wasu abokaina ne, amma bisa yadda rayuwa take babu aikin da ba za a fuskanci wata matsala ba. Allah ne Ya ba ni wannan shugabanci kuma ina ci gaba da dorawa bisa yadda wadanda suka gabace ni suka yi iya bakin kokarinsu na hidima ga al’ummar karamar Hukumar Katagum da Jihar Bauchi. An gyara wajen kula da marasa lafiya na wannan asibiti da wajen koyar da karatu da ya shafi likitoci da ungozoma da sassa daban-daban na asibitin. Akwai wani sashi da muka ware na jin dadin marasa lafiya a wannan asibiti na FMC, Azare duk marar lafiyar da ya zo wannan asibiti da wani korafi ko koke za mu zauna da shi domin jin abubuwan da suke faruwa. To amma muna fama da karancin kwarrun likitoci a asibitin, amma kuma muna ci gaba da aiki da wadanda muke da su. Muna matukar godiya ga mutanen garin Azare bisa yadda suke ba mu goyon baya a wannan asibiti ba mu da wata babbar matsala da ta sha kanmu a halin yanzu sai dai abubuwan da ba a rasa ba. Sannan ina kira ga duk wanda yake da wata hanya da zai taimaka wa wannan asibiti da kayan aiki ko wani abu da sibitin ke bukata ya zo ya taimaka, muna maraba lale da haka.
Gwamnati tana iya bakin kokarinta don ganin ta magance mana matsalolin da muke fuskanta, amma duk da haka masu hannu da shuni na wannan karamar hukuma suna ba da tallafi ga wannan asibiti daidai gwargwado.
Aminiya: Yaya dangantakarku da ma’aikatan asibitin?
Dokta Ibrahim: Ma’aikatan wannan asibiti suna ba da dukkan goyon bayan da ya kamata a matsayina na shugabansu kuma dukkan abubuwan da muke gudanarwa a fili muke yi, idan muna da matsala da mutum mukan fada masa ya gyara saboda haka ba ma wasa da batun hakkokin ma’aikatan wannan asibiti.
Aminiya: Ko akwai wasu daga cikin ’yan siyasa da suka taba kawo gudunmawa ga asibitin?
Dokta Ibrhaim: Akwai da yawa daga cikin manyan ’yan siyasa na wannan gari da suke ba da gudunmawar magunguna ga wannan asibiti. Misali akwai Dokta Musa Babayo Talban Katagum da ya kawo mana gudunmawar motar daukar marasa lafiya, wadda aka kiyasta kudinta kan Naira miliyan 10 zuwa 20. Bayan shi akwai Honarabul Ghali shi ma ya ba mu gudunmawar magunguna, akwai Alhaji kankani shi ma yana ba da tallafin kudade domin kula da marasa lafiya da sauran masu ruwa da tsaki na wannan karamar hukuma. Ina kira ga sauran ’yan siyasa su rika tallafa wa marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali a sassa daban-daban na Najeriya. Mata masu haihuwa da kananan yara suna samun tallafi a wannan asibiti kamar yadda wasu daga cikin kungiyoyi irin su TSHIP da makamantansu suke bayarwa. Kuma daga lokaci zuwa lokaci suna horar da ma’aikatanmu dabarun aiki na zamani. Gwamnatin Jihar Bauchi tana ba da gudunmawa ga wannan asibiti, misali bangaren da muke zaune hanzu haka gwamnatin jihar ce ta gina mana bayan haka ta ba mu motocin aiki.
Aminiya: Ko akwai matsalolin da wannan asibiti ke fuskanta?
Dokta Ibrahim: Akwai matsaloli da dama, daga ciki muna son inganta sabon wajen da muke ciki, kuma muna da karancin likitoci da ungozoma a asibitin nan. Bayan haka muna bakin kokarin horar da ma’aikata. Muna da kwararrun likitoci 12 a halin yanzu akwai wasu da ke kasa mutum 60, sai kuma mutum 10 da suke karatu sun kusa dawowa bakin aikinsu. A baya akwai masu bin wannan asibiti basussuka amma yanzu duk mun samu mun biya su hakkokinsu. Kuma ina tabbatar maka cewa duk likitan da muka kama yana musgunawa marasa lafiya muna daukar matakan da suka kamata a kansa.
Aminiya: Wane hali marasa lafiya da harin bam na kwanaki suke ciki?
Dokta Ibrahim: Bayan da abin ya faru an kawo mana wadanda suka yi rauni mutum 13 sai kuma mutum biyar da suka rasu, amma daga cikin wadanda suka samu raunin mutum uku sun sake rasuwa, saboda haka wadanda suka rasu a harin bam na Azare mutum takwas ne a halin yanzu. Mun sallami da yawa daga cikin wadanda suka samu raunin amma akwai saura mutum biyu, daya kafarsa ta yanke a lokacin da abin ya faru.