Jama’a na zaman zullumi kan sake zaben Gwamnan Taraba

Sake zabe a wasu mazabun Jihar Taraba ya jefa al’ummar jihar zullumi saboda tsoron abin da ka iya biyowa bayan zaben.  Wannan tsoro da mafi yawan al’ummar jihar musamman mazauna Jalingo fadar jihar ke nunawa na da nasaba da abin da ya biyo bayan zaben Gwamnan na 11 ga Afrilu inda akasamu asarar rayuka da […]

Jama’a na zaman zullumi kan sake zaben Gwamnan Taraba
Jama’a na zaman zullumi kan sake zaben Gwamnan Taraba

Sake zabe a wasu mazabun Jihar Taraba ya jefa al’ummar jihar zullumi saboda tsoron abin da ka iya biyowa bayan zaben. 

Wannan tsoro da mafi yawan al’ummar jihar musamman mazauna Jalingo fadar jihar ke nunawa na da nasaba da abin da ya biyo bayan zaben Gwamnan na 11 ga Afrilu inda aka
samu asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan jihar, wadanda suke da yanayi na addini da kabilanci.
A garin Jalingo wasu unguwanni dole al’ummar Musulmi suka kaurace wa gidajensu saboda barazanar da wasu matasan Kiristoci suka yi musu na neman hallaka su da kone gidajensu.
’Yan siyasa a jihar suna zargin kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar da Janar T.Y. danjuma (mai ritaya) da laifin hada rigima, domin tun farko Janar danjuma ya nuna cewa yana son Mista Darius Ishaku daga Kudancin jihar ya yi takaran Gwamnan Jihar. Daga bisani kuma kungiyar CAN reshen Jihar Taraba ta fito fili ta nuna goyon baya ga Mista Darius Ishaku.
Wannan matsayi na danjuma da kungiyar CAN bai yi wa wasu al’ummar jihar dadi ba domin a ganinsu haka zai iya hura wutar rigimar addini da kabilanci a jihar wadda ta dade tana fama da irin wadannan fitinu.
Wasu ma suna ganin kin rantsar da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar a matsayin Gwamna duk da rashin warkewar Gwamna danbaba Suntai an yi da gangan ne don a kawo Darius Ishaku wanda yaron danjuma ne.
dan takarar Gwamna a Jam’iyyar SDP, Mista Dabid Sabo Kente wanda Kirista ne dan kabilar Jukun daga yankin Wukari ya soki yadda danjuma da kungiyar CAN suka tsaya kai da fata cewa Darius Ishaku ne kawai dan takararsu kuma dole Kiristoci su mara masa baya.
Mista Sabo Kente ya ce bai kamata mutum mai matsayi a kasa kamar Janar danjuma ya nuna bambanci a tsakanin jama’ar jiharsa ba kamar yadda ya yi. Ya ce matsayin na Janar danjuma zai iya raba kawunan al’ummar jihar wadanda suka hada da Musulmi da Kirista da masu bautar dodo.
Mista Kente ya shaida wa manema labarai cewa ba zabe aka yi a yankin Wukari ba illa kawai an zauna an rubuta kuri’un da ake so aka bai wa PDP. Ya ce a Wukari an yi amfani da wurare biyu don tattara sakamakon zabe kuma ya kira Kwamishinan Zabe na Jihar ya fada masa abin da ke faruwa.
Mista Dabid Kente ya ce shi Kwamishinan Zaben ya fada masa cewa ya tafi wurin da ake karbar sakamakon zaben da bai cikin tsarin hukumar, ya ce da ya isa wurin sai ya iske motar yaki mai sulke kuma da sojoji suka gan shi, sai suka yi kansa ganin haka sai ya yi maza ya bar wurin don gudun kada a hallaka shi.
Ya ce yawan motocin yaki masu sulke da jami’an tsaro da aka tura yankin Wukari ko inda aka samu matsalar Boko Haram sai haka.
’Yar takaran Gwamna na Jam’iyyar APC, Sanata A’isha Alhassan ta yi watsi da sakamakon zaben baya, ta ce magudi ne kawai aka tafka a jihar. Ta yi zargin cewa jami’an hukumar zabe da jami’an tsaro sun hada baki sun yi magudi don ba PDP nasara a zaben.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa zabe a Taraba ya dauki salon addini da kabilanci wanda ya sa da yawa daga cikin jama’ar jihar kokarin kwashe iyalansu zuwa wasu jihohi don gudun faruwar hargitsi.