Jama’a su yi hattara da masu yi mana sojan gona – Shugaban IPMAN
Shuhaban kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa wato (IPMAN) reshen Jihar Adamawa, Alhaji Abubakar Abdullahi Butu ya yi kira ga al’umma da su yi hattara da wadanda ke wa kungiyar sojan gona. Shugaban ya ce: “Wannan jan-hankalin yana da muhimmanci saboda yadda suke samun rahotannin cewa akwai wani mutum da yake sojan gonan cewa shi […]
Shuhaban kungiyar Dillalan Man Fetur ta kasa wato (IPMAN) reshen Jihar Adamawa, Alhaji Abubakar Abdullahi Butu ya yi kira ga al’umma da su yi hattara da wadanda ke wa kungiyar sojan gona.
Shugaban ya ce: “Wannan jan-hankalin yana da muhimmanci saboda yadda suke samun rahotannin cewa akwai wani mutum da yake sojan gonan cewa shi ne shugaban kungiyar ta hanyar yada wata takarda da ke bayyana hakan,” inji shi.
Ya kara da cewa: “A matsayina na zababben shugaban kungiyar nan ba zan bari wani mutum ya kawo rudani a cikin kungiyar ba.”
Alhaji Butu ya ce jama’ar Jihar Adamawa da na Taraba kar su yadda su yi mu’amala da wannan kungiyar. “Ni da ’yan kungiyarmu 10 muka samu kujerunmu bayan anyi sahihin zabe don haka idan wani yana ganin cewa shi ne shugaban to ya bayyana alama ko wata takarda wadda za ta tabbatar wa jama’a cewa shi ne shugaban IPMAN.”
Ya ci gaba da cewa: “Bayan an zabeni, akwai sheda wato (Certificate) da kungiyar ta ba ni wanda na karba daga hannun tsohon shugaban IPMAN Alhaji Babakano Aliyu Jada”.
Daga nan shugaban ya karyata jita-jitar cewa mutumin ya samu damar zama shugaban IPMAN din jihar ne saboda hukuncin da Babban Kotun Jihar Fatakwal wanda ta yanke a ranar 20 ga Maris din bara, wanda kuma aka ce Mista Obasi Lawson ne Shugaban IPMAN na kasar baki daya. Ya ce wannan hukuncin da aka yanke bai shafe ofishinsu na Yola ba. Ya ce: “Kuma babu dan kungiya ko guda dake Yola da hukuncin ya shafa.”