Jama’a sun dawo da kayan da aka sace a zanga-zangar yunwa a Gombe
Al’ummar Bolari sun dawo da kayayyakin da bata-gari suka sace a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa
’Yan sanda sun jinjina wa al’ummar yankin Bolari da ke Jihar Gombe bisa yadda suka dawo da kayayyakin da bata-gari suka sace a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta yaba musu ne a lokacin da take sanar da kama mutum 90 kan zargin sace kayan jama’a a yayin zanga-zangar.
Rundunar ta kara da cewa an samu nasarar dawo da wasu kayayyaki masu yawa da aka sace a jihar ba tare da asarar rai ba.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Gombe, ASP Buhari Abdullahi, ya sanar da cewa a halin yanzu zaman lafiya ya dawo a jihar inda kowa ke ci gaba da gudanar da harkokinsa na yau da kullum.
- An sa dokar hana zirga-zirga tsawon sa’a 24 a Jos
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Gamsu Da Jawabin Tinubu Ba
- Amnesty ta buƙaci a binciki kisan masu zanga-zanga a Kano
Ya ja hankalin jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu, suna masu kara kulawa ta musamman da duk abin da su amince da shi ba.
A cewar sanarwar, dawowar zaman lafiya na nuna kwarewa, juriya, da hakuri da jami’an rundunar da sauran hukumomin tsaro suka yi a jihar.
Sannan ya ce kowa ya ba da gudummawa wajen wannan zaman lafiya, yana mai rokon jama’a da cewa su ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro wajen kiyayewa da tabbatar da doka da oda.