Jama’a sun hana ’yan bindiga shiga garinsu a Katsina
Jama’ar ƙauyen sun koka kan rashin zuwa jami’an tsaro a kan lokaci.
Taswirar Jihar Katsina
Mazauna ƙauyen Gurbi da ke Ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina sun hana ’yan bindiga shiga garinsu a yammacin ranar Lahadi.
Wani mazaunin ƙauyen wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun isa tun da wuri, amma mutanen gari suka taru sannan suka tare su, suka hana su shiga cikin ƙauyen.
Bayan da ’yan bindigar suka gaza shiga garin, sai suka juya kan mutanen da ke gudun tsira da rayukansu.
Sun harbe su tare da kashe aƙalla mutum 10.
“Yanzu haka akwai gawarwaki sama da 10 a yankin Nagodi, wani ƙauye da ke kusa da Gurbi. An dawo da gawarwakin zuwa Gurbi,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa tun kafin faruwar harin, al’ummar yankin sun sanar da jami’an tsaro bayan sun samu labarin cewa ’yan bindiga na shirin kai hari, amma ba a samu ɗaukin gaggawa ba sai bayan da aka kashe mutane.
“Mun sanar da jami’an tsaro tun da wuri, amma sai bayan harin ne suka iso domin kwashe gawarwaki,” in ji shi.
Wata majiya daga fadar shugaban al’umma ya tabbatar da cewa maharan sun kasa shiga ƙauyen, amma sun kai wa mutanen da suka tsorata suka fara gudu hari.
A baya-bayan nan dai, yankunan Kankara na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga.
Kwana uku da suka gabata, mahara sun kai hari Zangon Kankara, inda suka ƙone gidaje biyu da mota guda tare da yin garkuwa da mutane biyu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sanda da ofishin kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida na Jihar Katsina, ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.