Jama’a sun tsere zuwa gidajensu yayin harin Gudumbali a Borno
Jama’a da dama ne suka tsere zuwa gidajensu yayin da ake zargin wasu ‘yan Boko Haram sun kai hari a unguwar Gudumbali da ke karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno a yammacin jiya Talata, kamar yadda jami’an tsaron suka sanar. Maharan sun shiga garin ne da milsalin karfe 7:05 na yamma inda aka yi ta […]
Jama’a da dama ne suka tsere zuwa gidajensu yayin da ake zargin wasu ‘yan Boko Haram sun kai hari a unguwar Gudumbali da ke karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno a yammacin jiya Talata, kamar yadda jami’an tsaron suka sanar.
Maharan sun shiga garin ne da milsalin karfe 7:05 na yamma inda aka yi ta musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaron yankin.