Jama’a sun yi wa alkali bore a Saminaka

Daruruwan jama’a a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zanga dauke da kwalaye masu rubutun ‘Ba ma so’ da ‘Ba mu yarda ba,’ da ‘Ba ma son rashinadalci’ don nuna rashin amincewa da sake dawo da wani alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, mai suna Malam Haruna Aliyu Ya’u da aka fi sani da […]

Jama’a sun yi wa alkali bore a Saminaka
Jama’a sun yi wa alkali bore a Saminaka

Daruruwan jama’a a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna sun gudanar da zanga-zanga dauke da kwalaye masu rubutun ‘Ba ma so’ da ‘Ba mu yarda ba,’ da ‘Ba ma son rashin
adalci’ don nuna rashin amincewa da sake dawo da wani alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, mai suna Malam Haruna Aliyu Ya’u da aka fi sani da Mai Lullubi a ranar
Litinin din nan.
Masu zanga-zangar wadanda suka yi jerin gwano a cikin motoci da kan babura da masu tafiya a kafa, sun bi datse babbar hanyar da ta ratsa garin Saminaka tare da zuwa ofishin ’yan sandan garin da fadar Mai martaba Sarkin Saminaka da kotun da alkalin zai dawo ya ci gaba da aiki.
Masu zanga-zangar sun yi kukan cewa alkalin wanda ya shekara bakwai yana gudanar da alkalanci a Saminaka kafin a tada shi shekara biyu da suka gabata, ya yi wa al’ummar garin shari’o’i masu yawa na rashin adalci da suka hada da cin mutuncin mutane da kashe wa mata aure ba tare da bin ka’ida ba, tare da yin tarar makudan kudi kan abin da bai taka kara ya karya ba.
Shugaban kungiyar Matasan Saminaka da kewaye Malam Maiwada Ibarahim da ta shirya zanga-zangar ya ce a shekara bakwai da alkalin ya yi a garin mutane sun yi ta tsinuwa da tofin Allah tsine kan shari’o’in da yake yi.
Ya ce akwai shari’o’i da dama da ya yi, idan aka zo aka ce za a daukaka kara, a bayar da kwafin shari’ar da ya yi sai a ce babu. Ya ce matan aure sun mayar da kotun wajen sheke ayarsu, abu kadan sai su kai masa kara ya ci mutunci miji ya kashe aure.
Ya ce bayan haka ya yi ta daure mutane da yi wa jama’a tara ba bisa ka’ida ba. Akwai mutane sama da 100 da ya yi wa shari’o’i na zalunci a lokacin garin.
Shugaban ya ce ganin haka ya sa suka rubuta takardar kuka ga Babbar Jojin Jihar Kaduna a lokacin, inda aka tashi alkali daga garin.
Ya ce sai ga shi yanzu sun samu labarin an sake dawo da shi zuwa garin domin ya ci gaba da aiki.
“Don haka mu jama’ar Saminaka, muka fito baki daya muka gudanar da zanga-zangar lumana kan ba ma son alkalin ya dawo mana Saminaka. Mun rubuta takardar nuna rashin amincewa da dawo da alkalin mun bayar a fadar Sarkin Saminaka da ofishin ’yan sanda kuma za mu tura wa Alkalin Alkalan Jihar Kaduna da Gwamna da wuraren da suka kamata,” inji shi.
Ya ce suna da labarin an kai alkalin zuwa garuruwan Paki da Gubuchi da Kauru da dan Alhaji, amma mutanen garuruwan sun ki amincewa ya zauna a garuruwansu saboda
rashin adalcinsa.
Wakilinmu ya tuntubi Alkali Haruna Aliyu Ya’u (Mai Lullubi) ta waya, don jin ta bakinsa kan lamarin, sai ya ce, “Ban zan yi magana da kai ba, sai na samu izini daga manyana,” daga nan sai ya kashe wayarsa.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci ofishin Alkalin Alkalan Jihar Kaduna Dokta Maccido Ibrahim domin jin ta bakinsa a kan lamarin an ceya yi murabus, inda aka tura ta zuwa ofishin Akawun Kotun amma ba ya nan.
Da aka sake tura ta wajen shugabar ma’aikatan kotun, sai ta ce ba za su ce komai ba a yanzu ba, saboda suna shirin karbar sabon Alkalin Alkalai sai dai a dawo mako mai zuwa.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista