Jama’a sun yi zanga-zanga, sun nemi ceto a ceto mutum 176 da aka sace a Kwara
Jama’ar sun nemi ɗaukin gwamnatin tarayya kan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa yankinsu.
Ɗaruruwan matasa da mazauna Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin neman Gwamnatin Tarayya, ta ceto mutane 176 da aka sace a garin Woro kusan watanni shida da suka gabata.
Masu zanga-zangar sun ce mutanen sun shafe kwanaki 171 a hannun ’yan bindiga tare da roƙon gwamnati ta ceto.
- Venezuela ta sanar da ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya
- An yi jana’izar manoma 26 da aka kashe a harin ’yan bindiga a Zamfara
Sun yi tattaki a manyan titunan Kaiama ɗauke da alluna masu ɗauke da saƙonni tare da rera waƙoƙin haɗin kai.
Da yake magana a madadin masu zanga-zangar, Abdulhameed Abubakar, ya ce sun fito ne domin tunatar da gwamnati cewa har yanzu ba a ceto mutanen da aka sace ba.
Ya kuma buƙaci Shugaba Bola Tinubu, ya cika alƙawarin da ya yi na tura bataliyar sojoji zuwa Kaiama don tabbatar da tsaro.
Hakimin Woro, Umar Bio Salihu, wanda matarsa da ɗansa na cikin waɗanda aka sace, ya roƙi gwamnati da ta yi duk mai yiwuwa domin dawo da su gida lafiya.
Shugaban Ƙungiyar Ci Gaban Kaiama, Yakubu Salihu, ya ce al’ummar yankin na ganin kamar gwamnati ta yi watsi da su.
Ya ƙara da cewa hare-haren ’yan bindiga da sace-sacen mutane na ci gaba da aukuwa a yankin, ciki har da wani hari da aka kai kwanan nan a ƙauyen Aboki.
Shugabannin al’umma a yankin, sun kuma ce rashin kyawun hanyoyi na hana jami’an tsaro gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, inda suka buƙaci Gwamnatin Tarayya ta gyara hanyoyin yankin.
Da yake karɓar ƙorafin masu zanga-zangar, DPO na Kaiama, CSP Afiz Nafiu, ya tabbatar musu cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.