Jama’ar gari sun hallaka mai garkuwa da mutane a Sakkwato
Mutanen sun kashe wanda ake zargi da satar mutane suka kuma kona ofishin ’yan sanda.
Dan sandan kwantar da tarzoma (Tsohuwar ajiya).
Mutanen gari sun hallaka mutum daya da ake zargi da garkuwa da mutane suka kuma lahanta dayan a Jihar Sakkwato.
Dandazon mutanen sun kuma kona Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Kware ta Jihar inda aka tsare mutanen da ake zargi da satar mutane.
- ‘Jami’an gwamnati na wa jami’an tsaro manakisa a yaki da ta’addanci’
- An cafke Basarake da iyalansa kan zargin garkuwa da mutane
- Majalisa ta nemi Buhari ya ayyana dokar ta-baci a Najeriya
- Ronaldo ya gindaya sharadin rabuwa da Juventus
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce gungun mutane sun yi wa ofishin ’yan sandan tsinke ne suna neman a damka musu wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Kakakin Rundunar, ASP Abubakar Sanusi, ya ce ana tsaka da bincikar wadanda ake zargi ne mutane suka fara boren a ofishin ’yan sandan cewa dole a mika musu wadanda ake zargin.
Da haka ne zugar mutanen suka fi karfin jami’an da ke ofishin ’yan sandan, suka kona ofishin da motocin ’yan sanda da ke ajiye a wurin.
Ya tabbatar da cewa mutanen suna sun kashe daya daga cikin wadanda ake zargin, dayan kuma suka ji masa rauni.
Sai dai ya ce ba a kama kowa ba, amma ana kan gudanar bincike a kan lamarin.