Jama’a sun kona gawar dan fashin banki a Abuja
Al’ummar gari sun kona gawar wani dan fashi da makami a Karamar Hukumar Abaji da ke yannin babban birnin tarayya.
Al’ummar gari sun kona gawar wani da ake zargin dan fashin banki ne a Karamar Hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja.
’Yan fashin sun mamaye wani banki ne a garin bayan da farko sun kai farmaki ofishin ’yan sanda da ke kan hanyar Toto, inda suka harbe wani sifeto mai suna Abila.
Wani dan sanda ya ce a harin na ranar Alhamis ’yan fashin sun yi harbin kan mai uwa da wabi sannan suka zarce zuwa reshen bankin First Bank da ke kusa da wurin suka fara harbe-harbe.
Wani ma’aikacin bankin ya ce ’yan fashin ba su samu nasarar shiga cikin katafaren dakin ajiyar kudade ba, amma duk da haka sun yi awon gaba da wasu kudade daga saman kanta.
- Shari’ar Murja: Kotu ta umarci Hisbah ta Akawun Majalisar Kano su bayyana a gabanta
- NAJERIYA A YAU: Shin Mutum Zai Iya Cinye Naman Layyarsa Shi Kadai?
Ya ce maharan sun fara harbin wani mai gadi ne da ya shiga bandaki, kafin su shiga cikin bankin.
Daga bisanin tawagar hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji da ’yan banga da mafarauta suka yi gaggawar zuwa wurin inda suka yi arangama da ’yan fashin, suka kashe biyu daga cikinsu.
Wasu fusatattun mutane sun kwace daya daga cikin gawarwakin suka banka mata wuta.
Kwamishinan ’yan sandan Abuja, CP Benneth Igweh, ya tabbatar da cewa an harbe biyu daga cikin ’yan fashin ne a yayin musayar wuta da jami’an tsaro.
Ya ce an baza ’yan sanda masu yaki da ’yan fashi da makami da mafarauta a cikin daji domin gano wadanda suka gudu.
Haka kuma ya yaba wa kokarin jami’an tsaron wajen dakile harin sannan ya jajanta wa iyalan Sufeto Abila da ya rasu.