Jama’ar gari sun kona masu garkuwa da mutane

Mutanen sun kwace su a hannun ’yan banga sannan suka kona su kurmus.

Jama’ar gari sun kona masu garkuwa da mutane

Kone-konen da aka yi a zanga-zangar #EndSARS (Tsohuwar ajiya).

Wasu mutum biyar masu garkuwa da mutane sun bakunci lahira bayan jama’ar gari sun kona su kurmus.

Bayan masu garkuwar sun yi awon gaba da wasu matafiya ne ’yan banga suka cafke su, daga baya mutanen gari suka kwace su suka cinna musu wuta domin huce haucinsu kan yawaitar satar mutane a yankin.

Dubun masu garkuwar ta cika ne a kan hanyar Afuze zuwa Uokha a Karamar Hukumar Owan ta Yamma a Jihar Edo inda suka kama matafiyan suka tisa keyarsu zuwa cikin daji.

Ganin an kama su za a kai su ofishin jami’an tsaro, sai mutanen gari suka yi wa ’yan bangar taron dangi suka kwace masu garkuwar suka cinna musu wuta.

Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, Kontongs Bello, ya ce, “Bayan garkuwa da mutanen ne ’yan banga suka samu labari suka bi su, suka cafko su.

“A hanyarsu ta zuwa ofishin ’yan sanda a unguwar Uokha ne wasu fusatattun matasa suka kwace wadanda ake zargin da karfin tsiya suka kona su har lahira.”

Amma ya ce Rundunar ’Yan Sandan Jihar tana gudanar da bincike kan lamarin.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50