Jama’atu ba ta kyauta mana ba – ’Yan Shi’a
Gidauniyar Shi’a ta Rasulul A’azam (RAAF) da ke Kano ta bukaci kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta rika adalci a jagorancin da take yi ga sauran kungiyoyin Musulmi a Najeriya a matsayinta na uwa. Wata sanarwa da ta fito daga gidauniyar dauke da sanya hannun Kakakinta Malam Nasir Jafar, ta ce ba su ji dadin abin […]
Gidauniyar Shi’a ta Rasulul A’azam (RAAF) da ke Kano ta bukaci kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta rika adalci a jagorancin da take yi ga sauran kungiyoyin Musulmi a Najeriya a matsayinta na uwa.
Wata sanarwa da ta fito daga gidauniyar dauke da sanya hannun Kakakinta Malam Nasir Jafar, ta ce ba su ji dadin abin da Babban Sakataren Jama’atu Sheikh Khalid Abubakar Aliyu ya fada wanda jaridar Aminiya ta ruwaito a makon jiya ba, lokacin da yake gargadi ga malamai masu wa’azi su nisanci sukar juna, inda ya kebance ’yan Shi’a wajen nuna hadarin wa’azinsu.
“Babban Sakataren ya kebance ’yan Shi’a da wannan gargadi nasa inda jaridar ta ruwaito shi yana cewa: “daya daga cikin irin tafsirai masu hadari da suka bayyana shi ne na ’yan Shi’a wanda kuma aka rika yadawa ta gidajen rediyo da talabijin, kuma akidunsu na ci gaba da yaddwa a cikin al’ummar Musulmi..” Idan Sheikh Khalid bai kebance ’yan Shi’a su kadai a wannan gargadi ba, babu dalilin da zai sa mu yi korafi. Domin abin da ya yi gargadi a kai abu ne mai matukar muhimmanci a addinance da kuma hankalce. Saboda ayoyi da hadisai sun haramta furta magana mai tunzurarwa hatta ga wanda ba Musulmi ba,” inji gidauniyar.
Gidauniyar ta ce a yayin da take maraba da gargadin na Jama’atu da kuma duk matakin da hukuma za ta dauka don maganace matsalar tunzura jama’a, ta bukaci kungiyar ta Jama’atu Nasril Islam da kada ta bari wasu su yi amfani da sunanta mai daraja a idon Musulmin Najeriya wurin aikata rashin adalci ga wasu al’ummar Musulmin.
“Ba ma fata jagororin kungiyar Jama’atu su manta da babban makasudin da ya sa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya kafa wannan kungiya mai daraja, wato samar da hadin kan dukkan al’ummar Musulmin kasar nan,” inji sanarwar.